Sakon Buhari ga Musulmai a Ramadana: Ku guji a ingizaku zuwa raba kawunanku

Sakon Buhari ga Musulmai a Ramadana: Ku guji a ingizaku zuwa raba kawunanku

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na taya musulmai murnar shigowar watan Ramadana mai falala

- Ya kuma shawarci musulmai da su gujewa dukkan wasu kalamai da zasu tunzurasu zuwa raba kai

- Hakazalika ya kirayi musulmai da su tuna marasa karfi da rikici ya raba da gidajensu a cikin watan na Ramadana

Shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya yi maraba da fara azumin watan Ramadana wanda za a azumta na tsawon kwanaki 30, Daily Trust ta ruwaito.

A cikin sakon da ya aike wa 'yan kasar na Ramadan, Buhari ya roki Allah da ya karbi "sadaukarwar da muka yi ya kuma kara hadin kai, kaunar juna, zaman lafiya da ci gaban kasar."

KU KARANTA: Kuri'un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba, in ji Jonathan

Buhari ga musulmai a Ramadana: Ku guji a ingizaku zuwa maganar ballewa
Buhari ga musulmai a Ramadana: Ku guji a ingizaku zuwa maganar ballewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Buhari, a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bukaci musulmin kasar da su yi hakuri da juriya tare da yin watsi da muryoyin da ke neman raba kan al'umma.

Ya kuma bukaci dukkan 'yan kasa da su nuna jin kai ga miliyoyin marasa karfi kuma su tuna da wadanda rikici ya raba su da gidajensu da sadaukarwa da addu'oi a cikin wannan muhimmin lokaci.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sake kai farmaki yankin Kaduna, sun sheke mutane biyar

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Borno, Zulum, a ranar Litinin, ya jagoranci sanatocin da ke wakiltar jihar a majalisar dokoki ta kasa, suka ziyarci babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, da kuma shugaban hafsoshin sojan kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru a Abuja.

Zulum, sanata Kashim Shettima (Borno ta Tsakiya), Mohammed Ali Ndume (Borno ta Kudu) da Abubakar Kyari (Borno ta Arewa), tare da shugaban rikon Borno na APC, Ali Dalori, sun gana da shugabannin ne kan hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a wasu yankuna na jihar.

Dukkan ziyaran an yi su ne daban-daban kuma a cikin kowanne, an gudanar da tattaunawar ta sirri, Vanguard News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel