'Yan bindiga sun sake kai farmaki yankin Kaduna, sun sheke mutane biyar
- Rahotannin tsaro daga jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar wasu mutane biyar a wasu sassan jihar
- An bayyana cewa, mutanen sun mutu ne a wasu hare-hare daban-daban na 'yan bindiga a yankin
- Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ne ya bayyana faruwar lamarin
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Mista Samuel Aruwan ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyar a kananan hukumomin Zango-Kataf da Giwa a ranar Litinin, jaridar Punch ta ruwaito.
Kwamishinan a baya cikin wata sanarwa ya ce mutane biyu; uba da da, Joshua Dauda da dansa mai shekaru bakwai, Philip, a kauyen Wawan an kai musu hari a karamar hukumar Zangon-Kataf.
Duk da haka, yayin da yake sabunta rahoton, kwamishinan ya ce karin gawarwakin biyu jami'an tsaro sun gano su.
KU KARANTA: Zulum da Sanatocin Borno sun ziyarci CDS da COAS kan batun Boko Haram
"Bugu da kari ga bayanin farko kan harin da aka kai a kauyen Wawan Rafin da ke karamar hukumar Zangon Kataf, hukumomin tsaro sun bayar da rahoton cewa an gano gawarwakin wasu karin mutane biyu a yankin," in ji shi.
Aruwan ya bayyana wadanda lamarin ya rutsa da su da Francis Ayuba da wani karamin yaro, Florence Dennis, ya kara da cewa:
"Wannan ya kawo adadin wadanda suka mutu daga harin zuwa hudu, wadanda aka lissafa kamar haka: Joshua Dauda, Philip Dauda, Francis Ayuba da Florence Dennis."
Har ila yau, a wani labarin, kwamishinan ya ce ‘yan bindigar sun afka wa wata gonar rake a wajen Iyatawa a karamar hukumar Giwa suka harbe wani Isah Haruna, mazaunin yankin.
A cewarsa, hukumomin tsaro sun bayar da rahoton cewa an fatattaki gungun 'yan bindiga a Rugan Bello, wani matsuguni da ke kan hanyar Kajuru-Buda a karamar hukumar Kajuru ta jihar.
KU KARANTA: Kuri'un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba, in ji Jonathan
A wani labarin, Wasu rahotanni sun ce wasu gungun mutane sun kashe tare da kone wasu mutane uku da ake zargin ‘yan bindiga ne a garin Magamar Jibia da ke karamar hukumar Jibia a Katsina.
Lamarin ya faru ne lokacin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin da misalin karfe 11:25 na daren ranar Lahadi.
Wani mazaunin garin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ’yan bindigan sun kutsa kai cikin gidan wani mutum da ba a bayyana sunansa ba, wanda ya yi kukan kura mazauna garin kuma suka tattara suka yi wa 'yan bindigan kawanya.
Asali: Legit.ng