Magance tsaro: An kammala horar da 'yan sandan jiha 704 na jihar Kano

Magance tsaro: An kammala horar da 'yan sandan jiha 704 na jihar Kano

- An kammala horar da jami'an 'yan sandan jiha na jihar Kano akalla kimanin mutane 704

- Gwamna Ganduje ne ya taya su murna yayin da suka dawo daga makarantar horon a Kaduna

- Gwamna Ganduje ya kirayesu da su zama jajirtattu don tabbatar zaman lafiya a fadin jihar

Kimanin mutane 704 daga kananan hukumomi 34 na jihar Kano da aka zaba domin yin aiki karkashin shirin dan sandan jiha, an kammala horar dasu, jaridar Vanguard ta ruwaito,

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rukunin, wanda aka horar a Kwalejin ’Yan sanda da ke Kaduna, ya kunshi mutane 15 daga kowace daga cikin kananan hukumomin 44 na jihar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da ma'aikatan a Kano kuma ya taya su murnar kammala wannan horon.

Ya bukace su da su yi amfani da abin da suka koya wajen inganta tsaro a yankunansu.

KU KARANTA: Sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi ya kubuta, ya kuma hallaka 'yan bindiga

Magance tsaro: An kammala horar da 'yan sandan jiha 704 na jihar Kano
Magance tsaro: An kammala horar da 'yan sandan jiha 704 na jihar Kano Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

“Muna matukar godiya ga malamanku a Kaduna wadanda suka dage domin taimaka muku, kuma daga rahoton da muka samu, sun ce kun nuna halaye na kwarai.

“Kuma kun taka rawar gani, kuma suna sa ran za ku kara fiye da yanzu tunda kuna aiki ne don al’umma.

“Ko shakka babu tsaro babban kalubale ne a Najeriya, kuma ciki har da jihar Kano..

“Saboda haka, mun tsara wasu shirye-shirye da ayyuka da dama don tabbatar da cewa jiharmu ta samu tsaro.

“Dole ne mu godewa Allah da ya kare mu kuma ya sanya mu cikin daya daga cikin jihohi mafi aminci da zaman lafiya a cikin kasar nan.

"Dole ne mu ci gaba da yin addu'a ga Allah kuma a lokaci guda dole ne mu bi manufofinmu da nufin kare mutanenmu," in ji shi.

Ganduje ya ce aikin ‘yan sandan jiha ya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar nan, ya kara da cewa gwamnatinsa ta dauki matakin da muhimmanci.

KU KARANTA: A yau kasar Saudiyya za ta fara duban watan Ramadana mai zuwa

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ceto mutane 15 da aka sace tare da kwato shanu 32, The Nation ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Kaduna.

Jalige ya ce a ranar 9 ga Afrilu da misalin karfe 3:25 na yamma, wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar Buruku Birnin Gwari da ke kusa da dajin Unguwan Yako a kokarinsu na yin garkuwa da mutanen da ke cikin a motoci guda biyu kirar Volkswagen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.