Hukumar Sojin Najeriya ta saki hotunan Soji 11 da aka kashe a Benuwe
Hukumar Sojin Najeriya ta saki hotunan Sojoji 11 da wasu yan bindiga suka kashe a garin Banta na karamar hukumar Konshisha a jihar Benue makon da ya gabata.
A hotunan, an bayyana sunan kowani Soja cikinsu, rana haihuwarsa, ranar mutuwarsa da kuma addininsa.
Daily Trust ta ruwaito cewa gawarwakin jami'in soja daya da dakarun sojoji 11 suna kwance a makabartar a yanzu.
Manyan jami'an sojoji sun hallara wurin, suna jirar a fara yin jana'izar na sojojin.
A baya, rundunar sojojin ta sanar da cewa sojojin 11 da jami'in daya da aka kashe suna aikin samar da zaman lafiya ne tsakanin mutanen Bonta a Konshisha da Ukpute-Ainu a karamar hukumar Okay da ke rikici kan filaye.
Kalli hotunan:
Asali: Legit.ng