Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai

Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai

- Bincike ya bayyana adadin makudan kudade da gwamnatin tarayya ke tafka asararsu sakamakon aika-aikar fasa bututun mai a fadin Najeriya.

- A wani rahoto da aka hada, an gano biliyoyin da ake kashewa duk shekara a gyaran bututun mai da aka lalata a wasu sassan kasar.

- Rahoton ya kirgo wasu yankuna da lamarin fasa bututun yafi yawaita, yayin da NNPC ke koka irin asarar da hakan ke jawowa

Najeriya na kashe biliyoyin nairori duk shekara domin kula da bututun da ake amfani da su wajen jigilar mai, inda ake lalata daruruwan irin wadannan bututan a duk shekara, kamar yadda bayanan tuhuma da duba na Premium Times ya bayyana.

Kimanin bututun mai 1,161 aka lalata a fadin Najeriya a cikin watanni 21 tsakanin watan Janairun 2019 da Satumba na 2020, alkaluman da aka tono daga rahoton kudi na wata-wata na kamfanin mai na kasar, NNPC, ya nuna.

Barnar ta faru ne a bututan mai guda biyar a duk fadin kasar. Bututun yankin Port Harcourt shine mafi girma na "matattarar maki" a yanzu tare da maki sama da 538 da suka lalace.

Wannan ya biyo bayan bangaren Mosimi-Ibadan tare da maki 535 da suka lalace. Sauran bututun man sun hada da Gombe (46), Kaduna (32) da Warri-River Niger (10) sune suka biyo jerin ragowar satar bututun mai a kusan shekaru biyu.

Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai
Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai Hoto: premiumtinesng.com
Asali: UGC

Mafi yawan lalacewar wata-wata da aka gano a cikin ko wane yanki guda biyar asun faru ne a shekarar 2019, inda mafi girman lamarin ya kasance a watan Janairun 2019 tare da faruwar barnar sama da 230.

Na biyu mafi girma shine a watan Yulin wannan shekarar tare da barnar 228. Wannan ya biyo bayan barna 186 a cikin watan Satumba na shekarar 2019 da kuma 159 a cikin watan Agustan shekarar.

KU KARANTA: Sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi ya kubuta, ya kuma hallaka 'yan bindiga

Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai
Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A watan Satumbar 2020, lokacin da aka buga rahoton karshe, an lalata bututun mai 21, raguwar 43% cikin 100% daga maki 37 da aka samu a watan Agusta 2020.

Kafin wannan, a halin yanzu, kasar ta yi asarar fashin bututun mai 2,181 tsakanin watan Oktoba 2018 da watan Oktoba 2019.

"Satar kayayyaki da lalata bututun mai sun ci gaba da lalata abubuwa masu daraja da sanya NNPC a cikin hali mara kyau," in ji NNPC a daya daga cikin rahotannin.

Ko da yake barnar ta ragu a cikin 'yan watannin nan, amma tana ci gaba da illata lamuran kuɗi daga asusun gwamnati mara nauyi.

Daga watan Janairun 2019 zuwa watan Janairun wannan shekarar kadai, gyaran bututun da sauran kayan aiki sun ci kusan dala biliyan 15.

An kashe fiye da kashi ɗaya cikin uku na wannan adadin a cikin watanni biyu. A watan Mayun da ya gabata kamfanin NNPC ya kashe kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 200 wajen gyara. Kafin wannan, watan Maris 2020 ya lakume N2.6 biliyan don wannan aiki na gyara.

Kudin kulawa da Bututun

Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai
Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bincike na bayanan da aka samu daga rahoton FAAC na NNPC na wata-wata daga watan Disamba 2019 zuwa Janairu 2021 ya nuna cewa kamfanin ya kashe jimillar Naira biliyan 59.1 kan gyara da kula da bututun a cikin shekara guda.

Tsarin dabaru ya ci mafi girma na kudin a kan Naira biliyan 19.1. Gyaran bututun mai da sauran kayan aiki sun kai Naira biliyan 15; kason bangaren ruwa, Naira biliyan 10.9; tsaro da kulawa, Naira biliyan 8.9; da kuma kudin sarrafa bututun man, Naira biliyan 5.1.

Kudin da aka kashe akan bututun ya kasance mafi girma tsakanin Maris zuwa Mayu na 2019. A watan Mayu, an kashe N8 biliyan. A watan Afrilu kuwa ya kai Naira biliyan 7.8 da karshe watan Maris, Naira biliyan 7.7.

Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai
Rahoto: Biliyoyin kudin da Najeriya ke tafka asara duk shekara a gyaran bututun mai Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A watan Fabrairu, NNPC ta ce kasar tana asarar kimanin gangar danyen mai 200,000 a kowace rana na danyen man da take hakowa gida masu yin zagon kasa da kuma \masu aikata laifi ke yi.

Adadin da ya tashi daga ganga 70,000 a rana na danyen man da aka sata zuwa watan Agustan 2020.

A shekarar 2019, kungiyar NEITI, hukumar binciken man fetur ta kasa, ta fada a cikin wani rahoto cewa mambobin OPEC sun yi asarar kusan gangan danyen mai 138,000 a rana sanadin sata a cikin shekaru 10 da suka gabata na darajar dala biliyan 40.06.

KU KARANTA: Magance tsaro: An kammala horar da 'yan sandan jiha 704 na jihar Kano

A wani labarin, Mataimakin ko'odinetan al'ummar Hausawa a jihar Imo, Sulaiman Ibrahim Sulaiman, wanda aka fi sani da Garkuwan Hausawa, ya yi magana a wata hira da jaridar Punch game da kisan wasu mahauta bakwai a jihar da wasu 'yan bindiga suka yi.

Sulaiman ya bayyana cewa, babu shakka kisan Hausawan bakwai wani yunkuri ne na ta da zaune tsaye, musamman ma fada ta kabilanci, yana mai nuna takaicin irin wannan aika-aikata tare da mika wuya ga kaddarar Allah.

Da aka tambayeshi dangane da abinda ya fahimta a matsayin dalilin da yasa 'yan bindigan suka kashe mahautan, Sulaiman ya ce: "Kashe-kashen na da nasaba da siyasa. Ba shi da wata alaka da 'Yan asalin Biafra ko kungiyar tsaro ta Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.