Yanzu Yanzu: El-Rufai ya nada Usman a matsayin sabon Sarkin Kauru

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya nada Usman a matsayin sabon Sarkin Kauru

- Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya nada Alhaji Ya’u Shehu Usman, tsohon Sarkin Fadan Kauru, a matsayin sabon Sarkin Kauru

- Usman ya gaji marigayi sarki, Alhaji Ja’afaru Abubakar, wanda ya mutu a watan Janairun 2021

- Sabon sarkin ya kuma fito daga gidan sarautar Wadai

Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna ya amince da nadin Alhaji Ya’u Shehu Usman, tsohon Sarkin Fadan Kauru, a matsayin sabon Sarkin Kauru, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mista Muyiwa Adekeye, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, wanda aka bai wa manema labarai a ranar Asabar a Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Kyakkyawar budurwa ta gina gidanta kuma ta yi shafe da kanta

Yanzu Yanzu: El-Rufai ya nada Usman a matsayin sabon Sarkin Kauru
Yanzu Yanzu: El-Rufai ya nada Usman a matsayin sabon Sarkin Kauru Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce Usman, wanda ya fito daga gidan sarautar Wadai, ya gaji marigayi sarki, Alhaji Ja’afaru Abubakar, wanda ya mutu a watan Janairun 2021.

Usman, Shugaban Hukumar Kula da Kasafin Kudi ta Jihar Kaduna, an haife shi ne a ranar 15 ga Mayu, 1955 a Kauru kuma ya fara aiki da Ma’aikatan Jihar Kaduna a 1977.

Sabon basaraken ya yi ritaya a 2012 a matsayin Darakta, Ma’aikatar Kudi (MoFI), Ofishin Akanta Janar na Jihar Kaduna.

Akanta, Usman ya kasance tsohon Shugaban karamar Hukumar Giwa, Sakataren karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, kuma mai kula da Majalisar Karamar Hukumar Zangon Kataf.

Ya kuma kaance memba na Kwamitin mika mulki ta Jihar Kaduna kuma memba a hukumar bunkasa birane ta jihar Kaduna (KASUPDA).

KU KARANTA KUMA: Tsoffin Ministoci da wasu manyan yan siyasa biyar sun dawo PDP

A gefe guda, Sarkin masarautar Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya tsige Ciroman Zazzau Alhaji Sai’du Mai Lafiya daga kujerarsa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Sarkin ya tube rawanin Ciroman Zazzau ne saboda zargin rashin biyayya da girmama masarautar.

Ciroman Zazzau mai shekaru 84 a duniya ya kasance daga cikin manyan‘Yan Majalisar Sarki kuma Dan uwan Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ne na kut-da-kut.

A wani labarin kuma, Mai martaba Sarkin Lere, Birgediya Janar Abubakar Garba Mohammed (mai murabus) ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 77 a duniya.

Wata majiya daga garin na Lere da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa Legit.ng Hausa rasuwar sarkin.

Garba ya rasu ne a safiyar ranar Asabar 10 ga watan Afrilu a Kaduna bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel