Kyakkyawar budurwa ta gina gidanta kuma ta yi shafe da kanta

Kyakkyawar budurwa ta gina gidanta kuma ta yi shafe da kanta

- Wata matashiya ta zama abin birgewa a shafukan sada zumunta kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa ta gina kuma ta yi wa gidanta shafe da kanta

- Hotunan matashiyar da ba a san ko wacece ba sun bayyana tana aikin gini ba tare da an taimaka mata ba

- Da yawa sun bayyana ta a matsayin jarumar mata, yayin da wasu ke yabon ta

Wata matashiyar budurwa ta sha ruwan yabo a wajen mutane da dama bayan ta yi bajintar da ake ganin maza da yawa ne za su iya yi ba tare da taimakon kowa ba.

Matar da ba a gano ko wacece ba ta nuna gwaninta na yin bulo yayin da aka gano ta tana aikin gini da hafen gidanta ita kadai.

KU KARANTA KUMA: Tsoffin Ministoci da wasu manyan yan siyasa biyar sun dawo PDP

Kyakkyawar budurwa ta gina gidanta kuma ta yi shafe da kanta
Kyakkyawar budurwa ta gina gidanta kuma ta yi shafe da kanta Hoto: (@Ndi_Muvenda_)
Asali: Twitter

Da yake gabatar da aikin matar a Twitter @Ndi_Muvenda_ ya rubuta:

"Ba ta jira kowa ya taimaka mata ba ta gina gidanta da kanta kawai hafe ne ya rage.

"~ Ta fito ne Daga Makonde ~"

Mutane da yawa sun taya ta murna saboda abin da suka bayyana da halaye na jagoranci, wasu kuma suna ganin hakan abin ban mamaki ne.

Da yake mai da martani, wani mai amfani da shafin Twitter @RealGhost89 ya ce:

"Yawancin mata ba za su yi hakan ba ki ci gaba aikinki na kyau."

@Lekgowa_Kenna ya yi martani:

"Zan shigo ciki don in yi shafen gidan lambarta dan Allah."

MzizeNkosie ya ce:

"Gwarzuwa ce, na jinjina mata."

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Arewa sun bukaci IGP mai rikon kwarya da ya gaggauta kawo karshen ta’addanci

A wani labari na daban, an kama dalibin difloma na biyu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi saboda mallakar bindiga a harabar jami’ar.

Channels TV ta ruwaito cewa hukumomin tsaro sun bayyana dalibin a matsayin Shehu Mohammed, na sashin kula da harkokin gwamnati da lambar shiga makaranta 2018 / ND / PAD / 170.

Kafar yada labaran ya ruwaito cewa an samu bindiga da ake kerawa a cikin gida da kuma harsasai biyar a jikin dalibin a lokacin wani aikin bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel