Tsoffin Ministoci da wasu manyan yan siyasa biyar sun dawo PDP

Tsoffin Ministoci da wasu manyan yan siyasa biyar sun dawo PDP

- Tsoffin ministoci biyu, Jerry Gana da Humphrey Aba suna daga cikin manyan siyasa shida da suka koma PDP a Benuwe a ranar Asabar

- Farfesa Gana ya ce shi da sauran wadanda suka dawo sun yi matukar farin ciki da dawowa cikin jam'iyyar adawa bayan tsawon shekaru da yawa

- Tsohon ministan ya fadawa mambobin jam’iyyar PDP cewa ‘yan Najeriya suna tsammanin abubuwa da yawa daga jam’iyyar a 2023

An sake karbar tsohon ministan yada labarai, Farfesa Jerry Gana cikin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa an sake karbar Gana ne a ranar Asabar, 10 ga Afrilu a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Legit.ng ta tuna cewa Gana ya bar PDP ne a shekarar 2018 domin tsayawa takarar shugaban kasa a 2019 a karkashin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Tsoffin Ministoci da wasu manyan yan siyasa biyar sun dawo PDP
Tsoffin Ministoci da wasu manyan yan siyasa biyar sun dawo PDP Hoto: @RealJERRYGANA
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Arewa sun bukaci IGP mai rikon kwarya da ya gaggauta kawo karshen ta’addanci

Gana ya ce ya yi farin ciki da dawowarsa PDP kuma ya gode wa tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark da duk wadanda suka taimaka musu suka sami hanyar dawowa cikin jam’iyyar.

Tsohon ministan ya bayyana cewa akwai kyakkyawan tsammani a tsakanin 'yan Najeriya game da abin da jam'iyyar adawa za ta iya yi idan ta samu damar dawowa kan mulki a 2023.

Ya ce:

“Yan Najeriya suna sa ran za ku karbi ragamar mulkin kasar nan don shugabanci na gari da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar nan. Don haka ina kira ga jam’iyyar PDP da ta hada kai wuri guda kuma a hada kai domin ceto Najeriya da dawo da kyakkyawan shugabanci, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi tare da sanya kwarin gwiwa a zukatan ‘yan Nijeriya.”

KU KARANTA KUMA: Hankali ya tashi yayin da wasu da ake zargi 'yan fashi ne suka yi ruwan harsasai a kan sarkin Ekiti

Farfesa Gana bai dawo PDP shi kadai ba a ranar Asabar kamar yadda akwai wasu manyan ‘yan siyasa.

A wani labarin, tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana da magoya bayansa a jiya Laraba, 7 ga watan Afrilu, sun koma Jam’iyyar PDP.

Da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar a liyafar bikin dawowarsa PDP a hukumance a garin Bida da ke jihar Neja, Gana ya ce kasar nan ta tabarbare kuma tana bukatar ceto cikin gaggawa.

Gana, wanda mamba ne na kwamitin amintattu (BoT) na PDP a watan Maris, 2018, ya sauya sheka daga PDP ya kuma hade da jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel