Gwamnonin Arewa sun bukaci IGP mai rikon kwarya da ya gaggauta kawo karshen ta’addanci
- Gwamnonin Arewa sun yi martani game da nadin mukaddashin sufeto janar na ‘yan sanda, Usman Alkali
- Sarakunan na fatan cewa za a magance matsalolin rashin tsaro a kasar
- Yan bindiga sun mamaye wasu yankuna a arewacin kasar
Gwamnonin Arewa sun nemi mukaddashin sufeto janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Alkali, da ya zaunar da kasar nan lafiya.
Shugaban kungiyar, Simon Lalong, ya yi kiran ne a ranar Asabar, 10 ga Afrilu, a cikin sakon taya murna ga sabon shugaban ‘yan sandan, jaridar Premium Times ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Hankali ya tashi yayin da wasu da ake zargi 'yan fashi ne suka yi ruwan harsasai a kan sarkin Ekiti
Lalong a cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa, Makut Macham, ya ce Alkali ya cancanci wannan sabon matsayin duba da yadda ya yi wa kasar hidima.
Ya yi alkawarin cewa gwamnoni daga yankin za su ba da goyon bayan da ya dace ga mukaddashin Shugaban yan sandan, PM News ta ruwaito.
Gwamnan ya ce:
A matsayin mu na gwamnonin arewa, muna nan kan bakan mu na kula da harkokin 'yan sanda da duk wani matakin da zai kai mu ga tabbatar da tsaron yankin mu wanda yake fama da matsalolin rashin tsaro.
KU KARANA KUMA: Dattawan Arewa sun yanke hukunci: Sun amince da tsarin shugabancin karba karba
"Dole ne mu hada kai don daukar sabbin matakan da za su ba mu damar shawo kan wadannan kalubale kuma mu ci gaba da kasancewa a kan halin da ake ciki ta hana masu aikata laifuka aiwatar da munanan ayyukansu."
A wani labarin, Sheikh Ahmad Gumi, babban malamin addinin musulunci mazaunin jihar Kaduna ya ce ganin ƴan bindiga ya fi ganin Shugaba Muhammadu Buhari.
A cewar Dr Hakeem Baba Ahmed, kakakin kungiyar dattawan arewa, Gumi ya faɗawa masu ruwa da tsaki a yankin cewa ya daɗe yana ƙoƙarin ganin Buhari kan batun tabarɓarewar tsaro amma hakan bai yi wu ba.
Malamin addinin ya ziyarce dazuka daban-daban domin tattaunawa da ƴan bindigan da nufin kawo karshen hare-haren da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Asali: Legit.ng