An shiga firgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta

An shiga firgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta

- Wani dalibi na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi ya tsinci kansa cikin matsala sakamakon daukar bindiga da yayi zuwa makaranta

- Hukumomin tsaro na iya gurfanar da dalibin bayan sun kammala bincike kan lamarin

- Kungiyar asiri na daya daga cikin matsalolin tsaro da manyan makarantun Najeriya ke fuskanta

An kama dalibin difloma na biyu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi saboda mallakar bindiga a harabar jami’ar.

Channels TV ta ruwaito cewa hukumomin tsaro sun bayyana dalibin a matsayin Shehu Mohammed, na sashin kula da harkokin gwamnati da lambar shiga makaranta 2018 / ND / PAD / 170.

KU KARANTA KUMA: A nuna mana gawawwakinsu: Soja ya karyata ikirarin cewa an kashe mutum 70 a Binuwai

An shiga firrgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta
An shiga firrgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta Hoto: Abasiama Joseph/Facebook, @PoliceNG/Twitter
Asali: UGC

Kafar yada labaran ya ruwaito cewa an samu bindiga da ake kerawa a cikin gida da kuma harsasai biyar a jikin dalibin a lokacin wani aikin bincike.

A cewar PM News, Mohammed wanda ya zo rubuta jarabawarsa ta karshe ya yi yunƙurin guduwa a lokacin da jami’an makarantar suka nemi ya gabatar da kayansa don bincike.

Amma an kama shi tare da mika shi ga hukuma don ci gaba da bincike.

KU KARANTA KUMA: PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal

An yi amannar cewa ɗalibin ɗan ƙungiyar asiri ne kuma yana iya yin amfani da bindiga a lokacin da abokan karatunsa ke murnar kammala jarabawar ƙarshe.

A wani labarin kuma, Shugabannin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na yankin kudu maso yamma sun umurci mambobinsu suyi kaura daga jihar Ebonyi sakamakon kashe-kashen da akayi kwanakin nan.

An zargi Fulani Makiyaya da laifin kisan mutane akalla 15 a karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi a makon da ya gabata.

Kungiyar Miyetti Allah idan mambobinta sukayi kaura na dan lokaci, za'a samu zaman lafiyan da zai bawa jami'an tsaro daman gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel