Zan bar Kaduna da zaran na kammala wa’adin mulkina - El-Rufai

Zan bar Kaduna da zaran na kammala wa’adin mulkina - El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa da zaran ya gama wa'adin mulkinsa zai bar jihar Kaduna

- El-Rufai ya ce wannan ne dalilin da yasa gida daya kawai ya mallaka a jihar wanda ke a Unguwar Sarki

- Ya kuma bayyana cewar zai rage yawan ma'aikata a jihar musamman wadanda basu cancanta ba da kuma wasu da ya bai wa mukaman siyasa

Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya bayyana cewa zai bar jihar da zaran ya kammala wa’adin mulkinsa.

El-Rufai, wanda ya shekara biyu yana wa’adin sa na biyu, ya fadi haka ne a wata hira da aka yi da shi ta kafafen yada labarai ta gidajen rediyo.

Ya ce ya mallaki gida daya ne kawai a yankin Unguwar Sarki da ke cikin garin Kaduna saboda a karshen wa’adinsa, zai bar jihar.

Zan bar Kaduna da zaran na kammala wa’adin mulkina - El-Rufai
Zan bar Kaduna da zaran na kammala wa’adin mulkina - El-Rufai Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta rage ma’aikata daga cikin tsarin biyan albashi na jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Sarkin Zazzau ya tube rawanin Ciroman Zazzau

Ya kuma kara da cewa baya ga ma'aikatan gwamnati zai kuma rage yawan wadanda ya nada a mukaman siyasa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Bana satar kudaden gwamnati, bawai muna satar kudaden gwamnati bane don gina gidaje. Ina da gida ne a Unguwar Sarki kuma har zuwa yau shi ne gida daya tilo da na mallaka a Kaduna saboda bayan mulki na, ba zan zauna a Kaduna ba. Don haka, ba zan kara wani gida a jihar ba,” inji shi.

“Gwamnatin jihar ba za ta biya albashin mutanen da ba sa aiki ba, saboda haka, lamarin zai shafi ma’aikatan da basu cancanta ba da wadanda ke sama da shekaru 50 ciki har da wadanda ma ba sa zuwa aiki a kai a kai kuma duk da haka ana biyansu albashi."

Game da wadanda aka nada a mukaman siyasa, ya ce, “Muna duba yiwuwar rage nade-naden mukaman siyasa ne saboda idan ka rage wasu ka kasa rage naka, hakan zai zama rashin adalci. Tabbas za mu bincika mu rage wasu daga cikinmu a zahiri, tuni mun fara aiwatar da tsarin.”

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci

Ya shawarci wadanda abin zai shafa da su je su nemi wani aikin, yana mai cewa an zabe shi ne don yi wa mutanen jihar aiki kuma zai yi iya bakin kokarinsa.

A wani labarin kuma, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace ba zai baiwa wani mai garkuwa da mutane ko sisi ba koda kuwa dansa ne yake hannunsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hirar gidan rediyo da aka yi dashi ranar Juma'a akan yadda gwamnatinsa take bullo wa 'yan bindiga, Premium Times ta ruwaito.

El-Rufai ya dade yana bayyana yadda yake amfani da karfi wurin magance ta'addanci a jiharsa, kuma yana tsaye akan bakarsa. Ya maimaita a ranar Alhamis cewa babu wani dan ta'adda daya dace ya rayu a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel