Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci

Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi martani a kan wasu lamura da ke hana uwargidansa Aisha bacci

- Buhari ya bayyana Aisha a matsayin mace mai kirki da ke son kwatowa mata yanci da kuma tallafawa marasa galihu

- Ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwar uwargidan tasa wanda Hajjo Sani ta wallafa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tsokaci kan wasu batutuwan da ke hana uwargidansa, Aisha bacci.

A cikin littafin: ‘Aisha Buhari: Being Different’, na tarihin rayuwar Uwargidan Shugaban Kasar, Buhari ya bayyana matar sa a matsayin mace mai kirki.

Shugaban kasar ya ce batutuwan da suka shafi cin zarafin mata da kuma marasa karfi suna damun matarsa sosai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci
Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci Hoto: @aishambuhari
Asali: Twitter

Hajjo Sani, babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa kan sha'anin mulki da harkokin mata, ita ce ta wallafa littafin, wanda ya kasance tarihin rayuwar matar Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Zamfara kan sauya shekar Matawalle

"Wannan littafin" 'Aisha Buhari: Being Different' na Hajjo Sani, ya ba ni damar faɗin wasu abubuwa game da Aisha, matata, wacce na yi shekara 30 tare da ita da manyan yara biyar," in ji Buhari.

“Aisha kamar yadda duniya ta san ta tana da kirki; wannan saukaka tafiyarta na taimako da jin kai a lokacin da ta zama matar shugaban kasa. Hakanan halinta na kariya yana fassara kuzari na musamman da take nunawa yayin da ake cin zarafin mata, yara, da kuma marasa ƙarfi. Na lura da sha'awa sosai yayin da take magance yawancin matsalolin zamantakewar da suke hana ta bacci.

“Shirye-shiryenta, FUTURE ASSURED, ya samar mata da abin hawa na musamman don aiwatar da mafarkinta: isa ga gajiyayyu, marasa lafiya da iyalai marasa galihu don inganta jin daɗinsu, wani lokacin a yankuna masu nisa, musamman‘ yan gudun hijira.

“Matsayin da ta dauka na kare mata a cikin alumman mu a duk fadin kabilu mabanbanta, shima ya girmama sosai. Wannan yana taka muhimmiyar rawa a kokarinta na shiryawa da kuma daidaita mutane masu tunani iri ɗaya tare da manufa iri ɗaya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji sun kashe sama da mutane 70 da basu jiba basu gani ba, sun rusa asibitoci; Mazauna Benue

"Duk wadannan sun kara karfin gwiwa ga kokarin gwamnati na inganta rayuwar 'yan Najeriya ta hanyar tattalin arziki mai karfi da kuma kasar da ta cancanci kauna da alfahari da mu."

A wani labarin, Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bude baki tayi magana kan yadda ta rayu bayan tayi aure tun tana yar karamar yarinya.

Ta auri Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 1989 lokacin tana da shekaru 18 da haihuwa.

A cikin littafin: ‘Aisha Buhari: Being Different’, ma’ana “Aisha Buhari wacce ta zama daban” uwargidan shugaban kasar ta ce a lokacin da ta yi aure tana matashiya sai ta ga kamar akwai rashin tabbass kan makomarta a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel