Ko ɗan da na haifa aka sace ba zan biya kudin fansa ba, zan yi addu'ar shigarsa aljanna, El-Rufai

Ko ɗan da na haifa aka sace ba zan biya kudin fansa ba, zan yi addu'ar shigarsa aljanna, El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna yace ko sisinsa ba za tayi ciwo ba idan 'yan bindiga suka yi garkuwa koda kuwa da dansa ne

- Gwamna Nasir El-Rufai ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi dashi a gidan rediyo a ranar Juma'a

- A cewarsa ya dade yana shawartar iyalansa da su kula sosai don gudun fadawa hannun masu garkuwa da mutane

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace ba zai baiwa wani mai garkuwa da mutane ko sisi ba koda kuwa dansa ne yake hannunsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hirar gidan rediyo da aka yi dashi ranar Juma'a akan yadda gwamnatinsa take bullo wa 'yan bindiga, Premium Times ta ruwaito.

El-Rufai ya dade yana bayyana yadda yake amfani da karfi wurin magance ta'addanci a jiharsa, kuma yana tsaye akan bakarsa. Ya maimaita a ranar Alhamis cewa babu wani dan ta'adda daya dace ya rayu a duniya.

KU KARANTA: Al'amuran 'yan bindiga ke kashewa da dakile cigaban arewa, ACF

Ko ɗan da na haifa aka sace ba zan biya kudin fansa ba, zan yi addu'ar shigarsa aljanna, El-Rufai
Ko ɗan da na haifa aka sace ba zan biya kudin fansa ba, zan yi addu'ar shigarsa aljanna, El-Rufai. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Caccakar gwamnati ta fi ta'addanci da 'yan bindiga hatsari, Fadar shugaba Buhari

Akan hakan ne ya dade yana shawartar iyalansa da su kula kwarai don kada a yi garkuwa dasu. Yace ya dade yana bayyana musu cewa ba zai iya baiwa wani dan ta'adda ko sisi ba.

"Ina nan a kan bakata, kuma ina maimaitawa. Koda dana aka sace, zan dai taya shi da addu'ar samun shiga aljanna, amma sisi ta ba za tayi ciwo ba."

Da aka tambaye shi abinda gwamnatinsa take yi don ceto daliban FCFM Kaduna da aka sace tun watan Maris, cewa yayi gwamnati tana ta kokarin ganin ta fito dasu don su koma hannun iyayensu amma gwamnatin ba zata biya ko asin ba.

Iyayen daliban sun dade suna damun Gwamna El-Rufai don ya tattauna da masu garkuwa da mutane su sako musu yaransu.

A wani labari na daban, Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC, ya daki kwano a karo na biyu yayin gabatar da jawabi, The cable ta ruwaito.

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya kira Dolapo Osinbajo, matar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da "matar shugaban kasa".

Ya yi wannan kwafsawar ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake jawabi wurin kaddamar da 'Tarihin Aisha Buhari: Mace ta musamman'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel