Al'amuran 'yan bindiga ke kashewa da dakile cigaban arewa, ACF

Al'amuran 'yan bindiga ke kashewa da dakile cigaban arewa, ACF

- ACF ta ce ta'addanci yana kokarin dakatar da cigaban arewacin Najeriya

- Cikin 'yan watannin nan 'yan bindiga suna ta kai hari wuri-wuri a arewa

- Sun bayyana hakan ne a wata takarda ta ranar Alhamis a Kaduna

ACF ta ce ta'addanci ne abinda yake mayar da arewa baya. Dama an jima ana kai hari yankin arewa a cikin watannin da suka gabata, jaridar The Cable ta ruwaito.

A wata takarda wacce suka gabatar a ranar Alhamis a karshen wani taro da suka yi a Kaduna, inda kungiyar tace 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane ne suke mayar da arewa baya.

Audu Ogbe , tsohon ministan noma ne ya jagoranci taron.

KU KARANTA: Fitattun 'yan siyasa 10 a Najeriya masu sarautar gargajiya

Al'amuran 'yan bindiga ke kashewa da dakile cigaban arewa, ACF
Al'amuran 'yan bindiga ke kashewa da dakile cigaban arewa, ACF. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Dangane da rashin tsaro, kungiyar ta bayyana takaicinta ta yadda harkokin arewa da kuma na Najeriya gaba daya," kamar yadda kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe ya karanta.

"Kungiyar nan ta yi Allah wadai da ayyukan da 'yan ta'adda suke yi a arewa, inda yace kashe-kashensu ya yawaita duk da dan yankin ne yake shugabancin kasa.

"Kungiyar ta koka a kan yadda wasu suka jagoranci rura wutar tashin hankali ta bangaranci da addini a cikin wannan tashin hankalin da ake ciki."

Sannan sun tattauna akan yadda har yanzu wasu dalibai suke hannun masu garkuwa da mutane ba tare da gwamnati ta yi wani abu ba.

Sannan sun nuna takaicinsu kwarai akan yadda ake ware dukiyoyi ana biyan masu garkuwa da mutane wanda ko a musulunci basa aiwatar da ayyuka nagari. Kuma zasu yi amfani da dukiyoyin don cutar da al'umma.

KU KARANTA: DSS tayi martani akan zarginta da ake da tsarewa tare da azabtar da marigayin direban Buhari

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace shugaban karamar hukumar Okrika dake jihar Ribas, Honarabul Philemon Kingoli, a Fatakwal.

Wannan lamarin ya faru ne bayan an harbe tare da kashe wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne a wani otal dake Fatakwal.

Leadership ta tattaro cewa, Kingoli wanda cikin kwanakin nan ya rasa damar hayewa kujerarsa a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP, an sace shi ne a kan titin Peter Odili dake Fatakwal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng