Tinubu ya sake kwapsawa bayan ya kira Dolapo Osinbajo da 'matar shugaban kasa'

Tinubu ya sake kwapsawa bayan ya kira Dolapo Osinbajo da 'matar shugaban kasa'

- Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC ya kara kwafsawa cikin furucinsa a karo na biyu

- Tinubu ya kira uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo da "matar shugaban kasa"

- Ya daki kwanon ne yayin da yake jawabi a ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da tarihin Aisha Buhari

Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC, ya daki kwano a karo na biyu yayin gabatar da jawabi, The cable ta ruwaito.

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya kira Dolapo Osinbajo, matar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da "matar shugaban kasa".

Ya yi wannan kwafsawar ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake jawabi wurin kaddamar da 'Tarihin Aisha Buhari: Mace ta musamman'.

KU KARANTA: Da duminsa: Fusatattun 'yan siyasa ne suka dauka nauyin harin Imo, Uzodinma

Tinubu ya sake kwapsawa bayan ya kira Dolapo Osinbajo da 'matar shugaban kasa'
Tinubu ya sake kwapsawa bayan ya kira Dolapo Osinbajo da 'matar shugaban kasa'. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon shugaban 'yan sanda, Osinbajo

An yi taron ne a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja.

Yayin da Tinubu yake wa jama'a jawabi ya ce: "Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatansa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Mai girma matar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari; matar shugaban kasa, Dolapo Osinbajo."

Bayan ya daki kwanon, sai da Tinubu ya dan dakata na 'yan dakiku kafin ya cigaba da jawabinsa.

Dama Tinubu ya taba kwatankwacin hakan a ranar 29 ga watan Maris, inda yace a tura matasa miliyan 50 soja don su yi gyara akan lamarin tsaro.

Ya yi wannan furucin ne a Kano lokacin da yake shagalin cikarsa shekaru 69 da haihuwa.

Bayan yaduwar wannan jawabin nasa, ya yi gaggawar gyara akan kalamansa inda yace yana nufin matasa dubu 50 ba miliyan 50 ba.

A wani labari na daban, gwamnan jihar Borno, farfesa Babagana Umara Zulum ya kwana yana rabawa 'yan gudun hijura 70,000 Naira miliyan 200 da kayan abinci a ranar Laraba, kuma sai da ya tsaya ya tabbatar kowannensu ya samu.

Dama an dakatar dasu daga zuwa kasuwanni, gonaki da sauran wuraren neman kudi sakamakon rashin tsaron daya addabi jihar.

Sakamakon haka ne Zulum ya fara harkokin taimako da tallafawa a garesu. Ya jajirce kwarai wurin ganin ya samar da walwala da tsaro ga duk 'yan gudun hijira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng