Aisha Buhari: Rayuwar da na yi a gidan shugaba Buhari tun ina da shekaru 18

Aisha Buhari: Rayuwar da na yi a gidan shugaba Buhari tun ina da shekaru 18

- Hajiya Aisha Buhari, ta magantu a kan yadda ta rayu bayan tayi auren wuri

- An kulla aure tsakanin Aisha da Shugaban kasa Muhammadu Buhari tana da shekaru 18

- Uwargidan shugaban kasar ta ce a fari ta shiga zullumi na yadda makomarta zai kasance a matsayinta na yarinya karama amma ta cimma nasara saboda burin da ke zuciyarta

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bude baki tayi magana kan yadda ta rayu bayan tayi aure tun tana yar karamar yarinya.

Ta auri Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 1989 lokacin tana da shekaru 18 da haihuwa.

A cikin littafin: ‘Aisha Buhari: Being Different’, ma’ana “Aisha Buhari wacce ta zama daban” uwargidan shugaban kasar ta ce a lokacin da ta yi aure tana matashiya sai ta ga kamar akwai rashin tabbass kan makomarta a gaba.

Aisha Buhari: Rayuwar da na yi a gidan shugaba Buhari tun ina da shekaru 18
Aisha Buhari: Rayuwar da na yi a gidan shugaba Buhari tun ina da shekaru 18 Hoto: BBC.com
Asali: UGC

Ta ce amma kyakkyawan fatan da ke zuciyarta ya sa ta ci nasara kan tsoro da damuwar da ta shiga.

KU KARANTA KUMA: 2023: Ka hakura kawai, ka ba yankin kudu dama - Kungiyar APC ta fadawa Yahaya Bello

Da take bayyana Buhari a matsayin irin namijin da kowace mace za ta so ta aura, ta ce dabi'un dangin ta sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin ta cimma nasara.

Dr Hajjo Sani, babbar mai taimaka wa Shugaban Kasa ta musamman kan harkokin mata, ita ta wallafa littafin, wanda yake tarihin uwargidan Shugaban kasar ne.

“A kauyuka da dama a arewacin Najeriya, ba a daukar karatun yara mata a matsayin abu mai muhimmanci. A zahiri, auren wuri yana shafar kowasu yara mata takwas. A cewar UNICEF, an rahoto cewa daya daga cikin ‘yan mata bakwai za su haihu suna da shekara goma sha bakwai, hanya mafi sauki da za a yi bayanin wannan dabi’ar ita ce, ta kasance wata dabara ta rage nauyin da ke kan iyali.

“Ana kuma kallon hakan a matsayin hanyar kare mutuncin yara mata. Wani rahoto ya nuna cewa auren yara kanana ya fi faruwa tsakanin 'yan mata wadanda basu da ilimi sosai da talakawa, da kuma wadanda ke zaune a yankunan karkara."

Yanayin da ya gabata shine irin yanayin zamantakewar al'adun da aka haifi Aisha kuma ta taso a ciki. Tayi aure tun tana karama, a gareta, makomar rayuwarta ya zama mara tabbas, daily trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi - In ji tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zeezee

“Amma burin da ke cikin zuciyarta yana da yawa. Abin sha'awa, ƙaddara ta haskaka rayuwarta da wani salihin namiji. Ta auri irin namijin da kowace mace za ta so tayi rayuwa da shi, mutum ne mai matsayi da rikon amana. Kodayake wannan ya ɗora ta kai tsaye a kan tafarkin ɗaukaka, martabobin iyalinta sune mabudin tasiri a rayuwarta har zuwa yau.

“A shekarar 1989, matashiyar budurwar, Aisha Halilu, ta auri Muhammadu Buhari, wani Manjo Janar mai ritaya kuma tsohon Shugaban kasar Nijeriya na mulkin soja. Aure yana tafiya cikin sauri, cike da rashin tabbas. ya shawo kan ƙalubalen da kuma matsawa zuwa inda ba a sani ba yana da mahimmanci a cikin aure. Aisha, kamar kowace ‘ya mace da ta yi aure tun tana matashiya, ta fuskanci ƙalubalen zama cikakkiyar mace.”

A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya cikin manyan mutanen da suka hallara a dakin taro na gidan gwamnati, Abuja, wurin taron kaddamar da littafin Aisha, matar sa.

Littafin, “Aisha Buhari, Being Different”, babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin mulki da mata, Dokta Hajo Sani, ce ta wallafa shi.

Buhari, wanda a yanzu haka yake Landan domin duba lafiyarsa, ya samu wakilcin Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikatansa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng