Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Zamfara kan sauya shekar Matawalle

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Zamfara kan sauya shekar Matawalle

- Bayanai sun nuna cewa sabon rikici na neman kunno kai a jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara

- Hakan ya kasance ne sakamakon shirin sauya sheka da Gwamna Bello Matawalle na jihar keyi daga PDP zuwa APC

- An tattaro cewa jam'iyyar reshen jihar na ganin a mayar da ita saniyar ware a tattaunawar da shugabanninta na kasa ke yi da gwamnan

Wasu sabbin bayanai sun bayyana, cewa rikici na neman kunno kai a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara; kan jita-jitar sauya shekar Gwamna Bello Matawalle daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Wasu majiyoyi masu tushe a cikin jam’iyya mai mulki sun ce neman samun wa’adin mulki biyu a 2023 shine babban dalilin da ya sa gwamnan ke yunkurin komawa APC, PM News ta ruwaito.

Majiyar ta ce duk da cewa ba boyayyen abu bane cewa “ubangidan gwamnan ya kasance tsohon gwamnan jihar har sau biyu kuma ya bashi goyon baya ta bayan fage, an gaya masa (gwamnan) cewa babu tabbacin zarcewarsa idan ya kasance a cikin PDP.

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Zamfara kan sauya shekar Matawalle
Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Zamfara kan sauya shekar Matawalle Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: UGC

“Zamfara ta kasance ta Jam’iyyar kuma an fada masa karara cewa idan yana so ya tsaya takara kuma ya samu zarcewa, dole ne ya sauya sheka zuwa APC.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari: Rayuwar da na yi a gidan shugaba Buhari tun ina da shekaru 18

"An gaya masa, wani lokaci a shekarar da ta gabata cewa abin da ya fi dacewa a gare shi shi ne 'ya koma gida ya samu tikitin tsayawa takara a shekarar 2023."

Sai dai kuma, wata majiyar ta ce a yayin da aka kammala tattaunawa kan batun sauya shekar gwamnan zuwa APC a matakin koli na jam'iyyar, an mayar da babin jam’iyyar na jihar saniyar ware.

Bincike tare da shugaban jam'iyyar APC na jihar, karkashin jagorancin Alhaji Lawal Liman ya nuna cewa “ba a saka su cikin tattaunawar kawo gwamnan daga PDP zuwa APC ba.

“A gaskiya, gwamnan ya kasance tare da mu kafin ya koma PDP amma da sasantawar da shugabannin kasa suka fara, da zai fi kyau idan aka je da APC Zamfara a tattaunawar.

“Yanzu da muka samu zaman lafiya, me ya sa suke yi mana haka, mu da muka tsaya tsayin daka; duk da cewa wasunmu sun rasa damar da muka samu a 2019? ”

A wani labarin kuma, wata majiyar ta ce kamar yadda ya faru a yammacin Alhamis din, “har yanzu babu tabbass ko mataimakin nasa zai koma APC.”

Amma PDP ta sha alwashin rokon gwamnan da kada ya koma APC.

“Lokacin da Gwamnatin Tarayya ta haramta tashin jirage a Zamfara, PDP ta yi magana kuma ta tashi cikin tsaron jihar; cewa ba su da wani dalili da zai sa su sanya jihar a kan dokar hana zirga-zirgar jiragen sama.

KU KARANTA KUMA: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi - In ji tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Zeezee

“A matsayinmu na jam’iyya, a ko da yaushe muna tare da gwamna, amma ina tabbatar muku cewa gwamnoninmu suna kan lamarin; a yanzu haka da muke magana.”

A baya mun ji cewa jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya fara shirin komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kafin yanzu, akwai jita-jita game da sauya shekar Matawalle, wanda ya zama gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP, bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani na APC a Zamfara.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima, a shekarar da ta gabata ya bayyana cewa shirye-shirye na gudana kan komawar Matawalle APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel