Yanzu Yanzu: Sojoji sun kashe sama da mutane 70 da basu jiba basu gani ba, sun rusa asibitoci; Mazauna Benue

Yanzu Yanzu: Sojoji sun kashe sama da mutane 70 da basu jiba basu gani ba, sun rusa asibitoci; Mazauna Benue

- Al'umman Mbator a Shangev-Tiev na karamar hukumar Konshisha da ke jihar Benuwe sun zargi sojoji da kashe masu mutane 70 a wani mamaya da suka kai

- An tattaro cewa mamayar sojojin ya biyo bayan kwanton bauna da wasu mayaƙan yankin suka yi wa dakarunsu guda 11

- Tun farko dai an tura jami'an tsaro yankin ne domin kwantar da rikici tsakanin kauyukan Bonta na Mbator a Shangev-Tiev da Okpute-Ainu a karamar hukumar Oju

Mutanen Mbator a Shangev-Tiev na karamar hukumar Konshisha da ke jihar Benuwe a ranar Juma’a, sun yi ikirarin cewa akalla bayin Allah da basu ji ba basu gani ba guda 70 aka kashe a mamayar da sojoji suka kai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kauyukan Bonta na Mbator a Shangev-Tiev na karamar hukumar Konshisha da Okpute-Ainu a karamar hukumar Oju sun kwashe tsawon shekaru da dama suna rikici kan filaye wanda hakan ke sa a tura jami'an tsaro don kwantar da rikicin.

Sabon rikici ya ɓarke a tsakanin garuruwan biyu kwanaki biyar da suka gabata kuma wannan ya yi sanadiyar tura sojoji.

Yanzu Yanzu: Sojoji sun kashe sama da mutane 70 da basu jiba basu gani ba, sun rusa asibitoci; Mazauna Benue
Yanzu Yanzu: Sojoji sun kashe sama da mutane 70 da basu jiba basu gani ba, sun rusa asibitoci; Mazauna Benue Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Zamfara kan sauya shekar Matawalle

Sai dai kuma, , an zargi wasu mayaƙan yankin da yi wa sojoji 11 kwanton bauna, lamarin da ya yi sanadiyar da sojoji suka kai mamaya.

Da take jawabi a taron manema labarai a Makurdi, babban birnin Benuwai, a safiyar ranar Juma'a, wata kungiya mai suna Shangev-Tiev Assembly (STA), ta bayyana cewa sojojin sun lalata akalla wasu garuruwa 15 da ke kusa da su tun lokacin da aka fara kai hare-hare ta sama da kasa.

Wani Dattijo Tyoh Jude, wanda ya yi magana a madadin STA, ya ce, “Ya zuwa yanzu sojojin sun kona tare da rusa gonaki, makarantu, asibitoci da gidajen Bonta, Tse-Jembe, Tse-Anyom, Gbinde, Mbaakpur, Aku, Agidi, Gungul , Adoka, Guleya, Awajir, Shiliki, Achoho da Ullam a karamar hukumar Gwer, kuma har yanzu suna shirin yin hakan ga sauran garuruwan makwabta cikin karamar hukumar Konshisha.

“Sojojin Najeriya dauke da makami suna kashe mutanenmu da ba su ji ba basu gani ba da gangan. A yanzu haka, sama da mutane 70 ne aka ba da rahoton sun mutu kuma sama da mutane 100 sun ɓace, galibi mata, yara da tsofaffi kuma dubban daruruwa sun rasa muhallansu."

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari: Rayuwar da na yi a gidan shugaba Buhari tun ina da shekaru 18

Sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga lamarin don hana sojoji ci gaba da kashe-kashen jama’arsu ba tare da bata lokaci ba.

Sun kuma bukaci gwamnatin Jihar Benuwai da ta tabbatar da cewa an shata layi kan iyakar yankin da ke rikici.

Mun ji cewa wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe jami'in soja daya da dakarun sojoji 10 a jihar Benue a yayin da suka fita aiki kamar yadda rundunar Sojin Nigeria ta sanar.

Kakakin rundunar soji, Janar Mohammed Yerima ya ce da farko an ce sojojin sun bace amma daga bisani an gano gawarwakinsu a karamar hukumar Konshisha na jihar a sakon da ya fitar daren ranar Alhamis a shafinta na Twitter.

Sanarwar ta kara da cewa an kwashe gawarwarkin nan take sannan ana cigaba da bincike da nufin gano wadanda suka aikata wannan mummunan lamarin da nufin hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng