Ku tayani da addu'a, ina cikin kangin rayuwa har ina ji kamar na kashe kaina, Ummi Zeezee
- Tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim ta koka a kan halin da ta tsinci kanta na kuncin rayuwa
- Ummi Zeezee ta ce lamarin ya kai ga har ta kan ji kamar ta dauki rayuwarta
- Sai ta nemi kada wanda ya tambayeta ba'asi illa ta nemi a taya ta da addu'a
Fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta ce ta shiga kangin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.
A ranar Asabar, 3 ga watan Afrilu ne jarumar ta fadi hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram.
Ta ce: “A ‘yan kwanakin nan, na shiga matsanancin kuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kaina.”
Sai dai jarumar wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu ”Jinsi,” “Gambiza” da "Tutar So" ta ce kada kowa ya tambaye ta dalilin da ya sa take so ta aikata wannan danyen aiki.
Ta kara da cewa “Amma don Allah kada kowa ya tambaye ni dalili me ya sa, abin da nake bukata a gare ku shi ne, addu’a.”
KU KARANTA KUMA: Buhari ya nuna bakin ciki yayinda yake juyayin rashin kakakin Afenifere Yinka Odumakin
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da mabiya shafinta suka yi kamar haka:
ayna_idriss ta ce:
“Nashiga damuwa d tashin hnkli wanda nasan idan kikaji xakiga naki bawani abu bane koda bansan meyake damun kiba Ammah bantaba sawa araena xan iya kashe kaenaba dan Allah kicire wannan tunanin daga ranki Allah ya yaye miki da muwarki ya musanya miki d farin ciki.”
auwal.ahmad1 ya ce:
“Allah ya kawo sauqi a lamuranki.”
honey_glow_kano ta ce:
“Idan anyi addua batada amfani ai kinfi kowa sani, ba zamu hanaki ba amma kisani jahannama khalidina fiha abada.”
jeeiddarrh ta yi martani:
“Ki dage da istigfari ki yawaita zikiri Insha Allah zaki samu sassauci ki daina cewa zaki kashe kanki.”
ibrahimsaedu
“A fara tuna hukuncin wanda ya kashe kansa kafin aga rayuwa tayi zafi.”
Zeezee ta kasance daya daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da tauraronta ya haska a farkon jerin shekarun 2000.
Ta yi fina-finai da dama da fitattun jarumai irinsu Ali Nuhu, marigayi Ahmed S. Nuhu, Abba El Mustapha da Ibrahim Mai Shunku.
KU KARANTA KUMA: Bikin Ista: Ku yi addu’ar dawowar zaman lafiya, Atiku ga yan Najeriya
A gefe guda, yayinda gaba daya aka yarda cewa aure shawara ne mai daɗi da masoya ke ɗauka don ƙarfafa dangantakar su, ma'auratan sune ke da zabi kan yadda suke so taron bikinsu ya kasance.
Hotunan bikin auren wasu ma'aurata 'yan Najeriya sun haifar da zazzafan muhawara a shafukan sada zumunta.
A hotunan da @SIR_YUYU ya yada a shafin Twitter, yayin da ma'auratan da ba a san ko su wanene ba suka yi kyau a cikin kayan bikin aurensu masu launin kore, yanayin da amaryar ta bayyana ne ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu.
Asali: Legit.ng