Ke ce uwargidar Najeriya, Ba wanda zai sake tantama akan Haka, Tinubu ga Aisha Buhari
- Jagoran jam'iyya mai Mulki, Bola Tinubu, ya ce duk wani da yake tantama akan muƙamin uwar gidan shugaban ƙasa na mace ta farko to ya daina.
- A cewar jigon na APC aikin ta da hazaƙar ta kaɗai sun isa su baiwa duk wani mai tababa amsar da yake nema.
- Mutane da yawa na ganin cewa kundin tsarin mulkin ƙasar nan bai bawa uwargidan shugaban ƙasa wani muƙami ba a hukumance
Jagoran jam'iyya mai mulki APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce a yanzun duk wata tantama da wasu ke yi kan muƙamin mace ta farko an share ta.
Wasu na ganin cewa kundin tsarin mulkin ƙasar nan baisan da ofishin na mace ta farko ba, wanda uwar gidan shugaban ƙasa ke riƙewa.
KARANTA ANAN: Manyan alkawura 3 da IGP Baba ya daukar wa ‘yan Najeriya bayan kama aiki
Jagoran APC ɗin yace ayyukan da matar shugaban ƙasa, Aisha Buhari ke yi kaɗai ya isa ya kore duk wata tantama da wasu ke yi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Tinubu ya faɗi hakane a wajen ƙaddamar da littafin tarihin matar shugaban ƙasar wanda aka sama suna "Aisha Buhari; Being different" wanda babbar mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin mata, Dr Hajo Sani, ta rubuta.
Jigon jam'iyyar ta APC, wanda shine shugaba wajen taron ya ce:
"Kasan cewar ɗumbin abubuwan da matar shugaban ta cimmawa, babu wanda zai ƙalubalanci ofishinta daga yanzun."
"Idan zaku iya tunawa wasu mutane na ganin cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai bawa matar shugaban ƙasa wani muƙami ba a hukumance."
"Amma saboda hazaƙa, ƙoƙari da kuma ayyukan Dr.Mrs. Aisha Buhari ya isa ya share musu duk wata tantama da suke yi."
KARANTA ANAN: Wasu 'Yan Bindiga sun yi awon gaba da Shugaban ƙaramar hukuma a jihar Rivers
Tinubu ya ƙara da cewa uwar gidan shugaban ƙasan ta taka muhimmiyar rawa wajen ɗaga ƙasar nan ta kowanne fanni.
Ya ce ita ƙaɗai ce ta ɗaga muryarta wajen kiran mu da muzama na kwarai don ƙasar nan ta yi kyau.
Ta kuma taga murya da ayi gyara a harkokin mulki don kyautata goben talakawan ƙasar nan.
A wani labarin kuma Wata mai juna biyu ta sheƙe mijinta har Lahira bayan taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu
Wata mata mai ɗauke da juna biyu ta kashe mijinta har lahira bayan wata yar taƙaddama ta shiga tsakaninsu wadda takai su har ga faɗa
Matar dake da 'yaya takwas ta saba dawowa gida daga wajen aiki a makare, wanda hakan na ɓatawa mijin rai har takai ga ya gargaɗi matar tasa da ta bari.
Asali: Legit.ng