Wasu 'Yan Bindiga sun yi awon gaba da Shugaban ƙaramar hukuma a jihar Rivers
- Wasu ƴan bindiga da ba'a gane ko su waye ba sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Okrika dake jihar Rivers
- Rahotanni sun bayyana cewa an sace shugaban ne akan hanyar Peter Odili a Patakwal babban birnin jihar Rivers
- Sai dai har yanzun waɗanda suka sace mutumin ba su nemi kowa ba, domin neman a biya kuɗin fansar shugaban ba
Wasu ƴan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Okrika, Philemon Kingoli, a jihar Rivers ranar Laraba.
KARANTA ANAN: Kara farashin mai da kudin haraji zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro, Dangote
Yan bindigar sun sace Kingoli ne da sanyin safiyar ranar Laraba a kan hanyar Peter Odili dake Patakwal babban birnin jihar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Har ya zuwa yanzun da aka haɗa wannan rahoton babu cikakken bayani kan yadda aka yi aka sace shugaban ƙaramar hukumar.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa har yanzun waɗanda suka sace mutumin ba su tuntubi kowa don neman kuɗin fansa ba.
Mai magana da yawun yan sandan jihar ta Rivers, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Punch a ranar Alhamis da safe.
KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun sake kai hari ofishin ƴan sanda a Imo, sun sace guda, sun raunta wasu
Ya kuma kara da cewa hukumar su ta yan sanda ta yi duk abinda ya kamata don ganin an kuɓutar da wanda aka sace ɗin.
Haka zalika, wani rahoto na daban ya bayyana cewa an harbe mutane biyu har lahira a ranar laraba da daddare a wani layi dake tsohon garin Patakwal.
Sai dai ana zargin cewa wasu yan ƙungiyar asiri ne suka kai harin har suka kashe mutanen biyu.
Omoni ya ce bai samu rahoton kisan ba, amma zai tuntubi shugaban ofishin yankin da abun ya faru sannan ya faɗawa manema labarai.
A wani labarin kuma Wata mai juna biyu ta sheƙe mijinta har Lahira bayan taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu
Matar dake da 'yaya takwas ta saba dawowa gida daga wajen aiki a makare, wanda hakan na ɓatawa mijin rai har takai ga ya gargaɗi matar tasa da ta bari.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa a ranar da abun ya faru matar ta sake dawowa gida a makare, sai mijin ya ƙalubalanceta akan karya dokarsa, wanda hakan yasa ta caka mishi wuƙa.
Asali: Legit.ng