'Yan bindiga sun tare ayarin motocin sojoji, sun ƙwace N28m da makamai a Benue

'Yan bindiga sun tare ayarin motocin sojoji, sun ƙwace N28m da makamai a Benue

- 'Yan bindiga sun tare ayarin motocin sojoji a Benue, sun kwace makamai masu yawa da Naira miliyan 28

- Sojojin sun fito ne daga karamar hukumar Katsina-Ala suna hanyar zuwa karamar hukumar Oju da nufin kaiwa wasu sojojin dauki

- A halin yanzu an fara bincike kan lamarin duba da cewa tawagar sojojin da kudin duk sunyi batar dabo

'Yan bindiga sun kwace makamai masu yawa da zunzurutun kudi Naira miliyan 28 daga hannun wata ayarin motocin sojoji da suka afka wa a jihar Benue, Vanguard ta ruwaito.

Sojojin sun fito ne daga karamar hukumar Katsina-Ala suna hanyarsu na zuwa karamar hukumar Oju (mai nisan kilomita 171 daga Katsina-Ala) yayin da yan bindigan suka tare su a Konshisha a ranar Talata, wata majiya ta shaidawa The Gazette.

'Yan bindiga sun tare ayarin motoccin sojoji a Benue, sun sace N28m da makamai
'Yan bindiga sun tare ayarin motoccin sojoji a Benue, sun sace N28m da makamai. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Wani babban jami'in soja ya ce yan bindigan da suka kai wa sojojin hari sun kwace makamai da kudi N28m suka tsere da su a tsakar daren suka bi hanyar gabar rafin Benue.

KU KARANTA: Ku bada himma wurin samar da tsaro a maimakon zawarcin mu, Gwamnonin PDP ga APC

"Eh, yan bindiga sun sace makamai da kudi kimanin N28m daga hannun sojoji," a cewar babban sojan.

"Ana bincike a kan batun tunda hedkwatar rundunar sojoji ta samu rahoton afkuwar lamarin."

Baya a bayyanawa kafafen watsa labarai inda kudin ya fito ba da abin da za a yi da shi a lokacin hada wannan rahoton.

Tawagar sojojin da ke dauke da kudin da makaman, karkashin jagorancin A.T Adebayo sunyi batar dabo.

Majiyoyi sun ce ba a ga kowa ba a lokacin da aka tura wasu sojojin bayan samun sanarwar abin da ya faru.

KU KARANTA: Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

Ana shirin tura wata tawagar sojoji na musamman domin bin sahun sojojin da nufin ceto su a cewar majiyar.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin rundunar sojoji game da lamarin amma hakan bai yi wu ba.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164