Ku bada himma wurin samar da tsaro a maimakon zawarcin mu, Gwamnonin PDP ga APC

Ku bada himma wurin samar da tsaro a maimakon zawarcin mu, Gwamnonin PDP ga APC

- Gwamnonin jam'iyyar hamayya ta PDP sun shawarci jam'iyyar APC ta bada himma wurin magance tsaro a maimakon zawarcin yan siyasa

- Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da gwamnonin PDP suka kaiwa gwamnan Zamfara don masa jaje bisa gobarar kasuwar Tudun wada

- Gwamnonin na jam'iyyar PDP sun kuma bawa mutanen da gobarar kasuwar Zamfara ta shafa tallafin Naira miliyan 100

Gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, sun bukaci jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki ta mayar da hankali wurin rashin tsaro da ke bazuwa a sassan kasar ta dena zawarcin mutane, rahoton Vanguard.

Babban jam'iyyar hamayyar ta bayyana hakan ne a lokacin da kungiyar gwamnonin PDP ke bada gudunmawar Naira miliyan 100 ga wadanda gobara ta shafa a kasuwar Katsina.

Ku dena zawarcin mu, ku mayar da hankali wurin samar da tsaro: Gwamnonin PDP ga APC
Ku dena zawarcin mu, ku mayar da hankali wurin samar da tsaro: Gwamnonin PDP ga APC. @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Kelvin Ebiri, hadimin gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ne ya fitar da sanarwar bayan kungiyar gwamnonin ta ziyarci gwamnan jihar Zamfara, Dr Bello Matawalle a ranar Laraba a Gusau don masa jajen gobara.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bi dare sun sace shugaban kwamitin riƙo jam'iyyar APC a gidansa

Shugaban kungiyar kuma gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ne ya jagoranci sauran gwamnonin PDP da suka hada da Nyesom Wike na jihar Rivers, Oluseyi Abiodun Makinde na jihar Oyo, Darius Dickson Ishaku na jihar Taraba, Bala Mohammed na jihar Bauchi da Ahmed Fintiri na jihar Adamawa.

Gwamnan sokoton ya ce a maimakon tausayawa mutanen Zamfara da ke fama da kallubalen tsaro da kuma gobarar da ta faru a baya-bayan nan, gwamnatin APC ta bige da siyasantar da lamarin.

Tambuwal ya sanar da bada tallafin Naira miliyan 100 daga gwamnonin PDP zuwa ga mutanen Zamfara da gobarar kasuwar Tudun wada ta shafa.

KU KARANTA: Ganduje ya zabtare rabin albashinsa da na sauran masu riƙe da muƙaman siyasa

A bangarensa, gwamnan Rivers Nyesome Wike ya shawarci jam'iyyar APC ta mayar da hankali wurin warware matsalolin da ke adabar Nigeria ta dena zawarcin gwamnonin PDP.

"Dukkan mu mun san halin rashin tsaro da kasar ke ciki. A maimakon APC ta mayar da hankali wurin magance matsalar tsaro, abinda jam'iyyar ke yi shine yawo daga jiha zuwa jiha tana zawarcin mutane," wani sashi na jawabinsa.

Wike ya bukaci takwararsa na Zamfara ya dena damuwa da jam'iyyar APC da ke zarginsa da assasa rikici a jiharsa.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel