Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace wani basaraken Najeriya bayan ya halarci bikin aure
- A halin yanzu ba a san inda wani sarkin Imo, Eze Charles Iroegbu yake ba
- An daura alhakin batan basaraken gargajiyar kan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
- Lamuran satar mutane ya zama ruwan dare a Najeriya
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Eze Charles Iroegbu, Sarkin Umueze Nguru a karamar hukumar Aboh Mbaise da ke jihar Imo.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an sace basaraken tare da wasu shugabannin majalisar masarautar lokacin da suke a hanyarsu ta dawowa daga bikin aure a cikin jihar.
Jaridar ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun tare sannan suka karkatar da motoci uku da ke dauke da Eze Charles Iroegbu, da shugabannin majalisarsa.
KU KARANTA KUMA: Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba
Wata majiya ta ce satar babban basaraken da aka yi ya haifar da tsoro da firgici a cikin al'umma.
A cewar majiyar:
“Mai martaba da shugabannin majalisar zartarwar sa sun kasance a hanyarsu ta dawowa daga bikin aure a Mbano lokacin da aka sace su. Wannan abin mamaki ne kuma akwai tsoro da firgici a koina.”
Wata majiya ta fadawa jaridar The Nation cewa lamarin ya faru ne a sanannen mahadar bakwai da rabi a yankin Obowo na jihar.
KU KARANTA KUMA: 2023: Daga karshe Arewa ta bayyana matsayinta akan zaben shugaban kasa, tayi watsi da tasirin addini
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta Imo, Orlando Ikeokwu, ya ce ba zai iya tabbatar da satar ba.
A gefe guda, mun ji cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace shugaban karamar hukumar Okrika dake jihar Ribas, Honarabul Philemon Kingoli, a Fatakwal.
Wannan lamarin ya faru ne bayan an harbe tare da kashe wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne a wani otal dake Fatakwal.
Leadership ta tattaro cewa, Kingoli wanda cikin kwanakin nan ya rasa damar hayewa kujerarsa a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP, an sace shi ne a kan titin Peter Odili dake Fatakwal.
Asali: Legit.ng