Yanzu Yanzu: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba

Yanzu Yanzu: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba

- IGP Usman Alkali Baba ya kama aiki gadan-gadan a matsayin sabon shugaban ‘yan sandan Najeriya

- Cire tsohon IGP, Mohammed Adamu, ya zo wa yawancin ‘yan Najeriya a bazata

- Adamu yana da kimanin wata daya da yayi masa saura na karin wa’adin shugabancinsa lokacin da aka cire shi

Sufeto janar na 'yan sanda mai barin gado (IGP), Mohammed Adamu, ya mika shugabanci ga sabon IGP mai rikon kwarya, Usman Alkali Baba.

A cewar jaridar PM News, an gudanar da bikin mika shugabancin ne a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Laraba, 7 ga Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fursunoni sama da 80 da suka tsere sun koma cibiyar gyara hali da ke Imo

Yanzu Yanzu: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba
Yanzu Yanzu: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba Hoto: @ProfOsinbajo
Asali: Twitter

Jaridar The Nation wacce ita ma ta ruwaito rahoton ta bayyana cewa Adamu ya mika mulki bayan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya yiwa Baba ado da sabon mukamin sa a Fadar Gwamnati, Abuja.

Da farko Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yiwa sabon Sifeto Janar na yan sanda kwalliya da karin girma zuwa IGP.

Za ku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya amince da nadin Usman Alkali Baba a matsayin sabon shugaban yan sanda.

Wadanda ke hallare a bikin kwalliyar sun hada da IGP mai barin gado, Mohammed Adamu; Sakataren gwamnati, Boss Mustapha; da Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi.

KU KARANTA KUMA: Lokacin da kudinmu ke da daraja: Yan Najeriya yi zazzafan martani yayin da hotunan tsoffin naira suka bayyana

Sauran sune Malam Garba Shehu; Laolu Akande; Sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar da sakataren ma'aikatar yan sanda.

Mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya.

Ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare.

Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya, maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng