‘Dan Majalisar Neja ya kawo kudirin da zai halattawa Musulmai amfani da Hijab a gidan Soja

‘Dan Majalisar Neja ya kawo kudirin da zai halattawa Musulmai amfani da Hijab a gidan Soja

- An kawo wani kudirin da zai bada damar amfani da Hijab a aikin Khaki

- ‘Dan Majalisar jihar Neja, Saidu Abdullahi ya gabatar da wannan kudirin

- A halin yanzu wasu masu amfani da hijab na fuskantar adawa a Najeriya

Wani kudiri da ke gaban majalisar wakilan tarayya ya na neman halattawa mata amfani da hijabi a wajen aikin gidan soja da sauran aikin khaki.

Jaridar Punch ta bayyana cewa Honarabul Saidu Abdullahi mai wakiltar Bida/Gbako/Katcha a majalisar wakilan tarayya ne ya gabatar da kudirin.

Wannan kudiri ya samu karbuwa, har ya kai mataki na biyu a zauren majalisar wakilan kasar.

KU KARANTA: Kotu ta yanke hukunci kan asalin Atiku Abubakar - Kungiya

Saidu Abdullahi wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin tattalin arziki ya yi wa kudirin take da: ‘Religious Discrimination (Prohibition, Prevention)’

Sashe na 13 na kudirin zai bada damar duk macen da ta ke bukata, ta rika amfani da hijabi, ba tare da an tsangwame ta a gidan soja ko wurin aiki ba.

“Duk wanda aka dauka aikin jami’in tsaro a gidan soja ko makamancinsu, ba zai gamu da tsangwama saboda zabin koyarwar addininsa ba.”

‘Dan Majalisar Neja ya kawo kudirin da zai halattawa Musulmai amfani da Hijab a gidan Soja
'Yan Majalisar Tarayya a zaure
Asali: Twitter

Rahoton ya ce kudirin zai halatta amfani da tambarin addini, kallabi (‘dan-kwali) da kuma hijabi.

KU KARANTA: Zaman makokin mutuwar Odumakin mu ke yi ba ta 2023 ba - Afenifere

Idan kudirin ya samu karbuwa, za a hukunta duk wanda aka samu da laifin tsangwamar masu sanya hijabi, amma kudirin bai tsaida hukuncin laifin ba.

Kudirin da ke neman samun shiga ya ba manyan kotu damar hukunta masu tsangwama, sannan hukumar NHRC za ta rika sauraron korafin jami'an tsaro.

Kwanakin baya kun ji sai da Ma'aikatar ilimi ta jihar Kwara ta sake garkame makarantu 10 da ta ba damar budewa saboda rikicin da ake yi game da sa hijabi.

Gwamnatin jihar Kwara tace ta yi hakan ne saboda lamarin tsaro sakamakon rikicin da ake yi saboda kotu da gwamnati sun bada damar sa hijabi a makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel