Yanzu-yanzu: Osinbajo ya rantsar da sabon Sifetan Yan Sanda, Alkali
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yiwa sabon Sifeto Janar na yan sanda kwalliya da karin girma zuwa IGP.
Za ku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya amince da nadin Usman Alkali Baba a matsayin sabon shugaban yan sanda.
Wadanda ke hallare a bikin kwalliyar sun hada da IGP mai barin gado, Mohammed Adamu; Sakataren gwamnati, Boss Mustapha; da Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi.
Sauran sune Malam Garba Shehu; Laolu Akande; Sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar da sakataren ma'aikatar yan sanda.

Source: Facebook
Source: Legit
Tags: