Ta bayyana: Rigingimu 3 da suka tilastawa Shugaba Buhari tsige IGP Adamu

Ta bayyana: Rigingimu 3 da suka tilastawa Shugaba Buhari tsige IGP Adamu

Korar Mohammed Adamu a matsayin Sufeto-Janar na ’Yan sanda (IGP) da aka yi a ranar Talata, 6 ga Afrilu, ya ba’ yan Najeriya da yawa mamaki.

An kori shugaban 'yan sandan ne bayan ya kwashe kimanin watanni biyu daga cikin karin wa'adin watanni uku da aka yi masa.

Ministan harkokin ‘yan sanda ya sanar cewa Mataimakin Sufeto-Janar na’ Yan sanda (DIG) Usman Baba, zai maye gurbin Adamu a matsayin IGP na riko, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya

Ta bayyana: Rigingimu 3 da suka tilastawa Shugaba Buhari tsige IGP Adamu
Ta bayyana: Rigingimu 3 da suka tilastawa Shugaba Buhari tsige IGP Adamu Hoo: Femi Adesina
Asali: Facebook

Da aka tambaye shi kan dalilin da ya sa shugaban kasa bai bar IGP mai barin gado ya kammala karin wa’adinsa ba, Ministan ya ce hakkin Shugaba Buhari ne yanke shawara kan lokacin da zai yi nadi.

Ya ce:

Shugaban kasa yana sane da wannan kuma ba za ku iya ɗauke masa wannan alhakin ba; shi ne wanda ke da alhakin nadawa ko tsawaita wa'adi. ''

Sai dai kuma, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa akwai wasu dalilai guda 3 da suka ja hankula wadanda suka sa shugaban ya kori IGP Adamu kamar yadda aka tattauna a kasa.

1. Karar da ke kalubalantar karin lokacin da aka yi wa IGP Adamu mai cike da rudani

A cewar jaridar Daily Trust, wasu majiyoyi masu tushe da ba sa so a ambaci sunan su sun yi ikirarin cewa daya daga cikin dalilan da ya sa aka kori tsohon IGP din shi ne saboda karar da ke kalubalantar karin wa’adin watanni uku da aka yi masa.

Lauya, Maxwell Okpara ne ya shigar da karar da ke kalubalantar ci gaba da kasancewar Adamu a ofis a gaban Babban kotun Tarayya da ke Abuja.

Majiyoyi sun ce fadar shugaban kasa ta yanke shawarar sauke shugaban 'yan sanda daga aikinsa ne domin ceton kanta daga kunci kan hukuncin kotun da ke gab da sabawa wa'adin.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye

2. Zargin barnatar da kudi da tabarbarewar lamura a hukumar 'yan sanda

Wani dalilin da ya sanya aka kori Adamu shi ne labarin da Daily Trust ta rahoto wanda ya yi zargin cewa rashin kyakkyawan tsarin tafiyar da harkokin kudi da tabarbarewar lamura na shafar ayyukan ‘yan sanda a duk fadin kasar.

Wata majiya a ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta ce labarin ya haifar da da mai ido yayin da fadar shugaban kasa ta nuna rashin jin dadinta ga hukuma da kuma ma’aikatar yan sanda.

3. Karuwar hare-hare kan hukumomin ‘yan sanda a kudu maso gabas

Jaridar ta kuma ruwaito cewa harin da aka kai hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Owerri, jihar Imo, da sanyin safiyar Litinin, 5 ga Afrilu, ya kai ga korar Adamu.

A cewar Sahara Reporters, wata majiya da ta yi magana ba tare da sunanta ba ta ce mutanen da ke kusa da shugaban kasar na hasashen cewa Adamu ya rasa dabara game da yadda za a dakatar da karuwar hare-haren da ake kaiwa kan ‘yan sanda a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.

A gefe guda, Sanata Shehu Sani ya mayar da martani game da korar tsohon Sufeto-Janar na 'yan sanda, IGP, Mohammed Adamu.

Sani, tsohon dan majalisar dattijai mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya bayyana ra'ayinsa ta shafinsa na Twitter a ranar Talata, 6 ga watan Afrilu.

Sani na hannunka mai sanda ne ga wani jawabi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba yi game da tsohon IGP din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel