Shehu Sani ga tsohon IGP: Sai wata rana Adamu, ka huta sosai don ka ciko daga ramar da kayi
- Sanata Shehu Sani ya mayar da martani game da korar da aka yiwa Mohammed Adamu a matsayin shugaban ‘yan sandan Najeriya a ranar Talata, 6 ga Afrilu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Adamu yayin da ya kai ziyarar aiki jihar Imo
- Sanata Sani na ganin yanzu Adamu zai iya dawo da jikinsa da ya rasa a matsayin IGP, inda yake hannunka mai sanda ga wani furuci da Buhari ya yi a baya
Sanata Shehu Sani ya mayar da martani game da korar tsohon Sufeto-Janar na 'yan sanda, IGP, Mohammed Adamu.
Sani, tsohon dan majalisar dattijai mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya bayyana ra'ayinsa ta shafinsa na Twitter a ranar Talata, 6 ga watan Afrilu.
KU KARANTA KUMA: Mallam dogo: Baiwar tsayi da Allah yayi wa wani saurayi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya
A takaice ya rubuta:
“Sai wata rana Adamu. Ka huta sosai sannan ka ciko daga ramar da ka yi.”
Sani na hannunka mai sanda ne ga wani jawabi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba yi game da tsohon IGP din.
Ku tuna cewa a watan Mayu 2019, Shugaba Buhari ya ce Adamu yana aiki tukuru don magance matsalar rashin tsaro a kasar wanda hakan ya sanya shi rage kiba.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne bayan ya dawo daga ziyarar kwanaki 10 da ya kai kasar Ingila.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye
A gefe guda, mun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yiwa sabon Sifeto Janar na yan sanda kwalliya da karin girma zuwa da IGP.
Za ku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ta amince da nadin Usman Alkali Baba a matsayin sabon shugaban yan sanda.
Wadanda ke hallare a bikin kwalliyar sun hada da IGP mai barin gado, Mohammed Adamu; Sakataren gwamnati, Boss Mustapha; da Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi.
Asali: Legit.ng