Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye

Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye

- Gwamnatin jihar Borno karkashin Farfesa Babagana Umara Zulum, ta bada umarnin gina gidaje 500 a Nguro Soye, Bama

- Yankin Bama shine karamar Hukumar da za a sake tsugunar da yan gudun hijaran da tashin hankali ya raba da muhallinsu

- Har ila yau za a gyara gidaje masu zaman kansu guda 1,000 a cikin garin wadanda maharan suka lalata

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bada umarnin gina gidaje 500 a Nguro Soye, Bama. Karamar Hukumar da za a sake tsugunar da yan gudun hijiran da tashin hankali ya raba da muhallinsu.

Bugu da kari, za a gyara gidaje masu zaman kansu guda 1,000 a cikin garin wadanda maharan suka lalata, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Azumin Ramadana: Saudiyya ta hana sahur da buda-baki a masallatan ƙasar

Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye
Gwamna Zulum ya gina gidaje 500 ga 'yan gudun hijira a Nguro Soye Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin ziyarar da ya kai garin Bama a jiya Talata. Yayin da yake a fadar Shehun Bama, Shehu Umar Ibn Kyari Ibrahim El-kenemi, Zulum ya yi alkawarin kara samar da damar samun ilimin ga duk yaran da suka isa makaranta.

Gwamnan ya kuma amsa tayin shehun Bama na karin tallafin noma ga manoma gabanin lokacin damina.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Babban hafsan sojin sama ya bayyana lokacin da ta'addanci zai zo karshe a Najeriya

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin yan fashi ne sun kashe mutane takwas sun jikkata wasu huɗu a wasu hare-hare da suka kai a yankin ƙaramar hukumar Ƙajuru da Kachia.

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Mr. Samuel Aruwan, ya tabbatar da kisan mutanen a wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Kaduna.

Aruwan ya ce ɗaya daga cikin harin shine wanda yan bindigar suka tare hanyar Kaduna zuwa Kachia, a dai-dai ƙauyen Kaɗanye dake ƙaramar hukumar Kajuru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel