Matashin da ya aura mata 2 a rana daya ya bada labarin romon amarcin da yake kwasa
- Dan Najeriyan nan da ya auri mata biyu a rana daya ya bayyana yadda al'amura suke gudana a gidansa a halin yanzu
- Mutumin mai shekaru 37 yace duk wasu abubuwa na so da kauna da yake samu suna nunkuwa ne kullum
- Ya baiwa samari kwarin guiwar auren mace fiye da guda wanda yace hakan yana hana wata a waje ta tafi da hankalin namiji
Babangida Sadiq Adamu, mutumin da ya auri mata biyu a rana daya ya bayyana yadda rayuwar aurensu take tafiya.
Dama labarinsa ya watsu a kafafen sada zumunta inda kowa ya tofa albarkacin bakinsa.
A wata tattaunawa da BBC Pidgin suka yi dashi ya bayyana yadda yake samun nishadi tun da ya auri mata biyu.
A cewar Adamu, yana samun morewar da tafi ta wanda ya auri mace daya. Yace duk wani jindadi da yake samu yana nunkuwa ne sakamakon auren mata biyu.
KU KARANTA: Zakakuran sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda 7 da suka kaiwa tawagar Zulum hari
An daura aurensa da matansa a ranar 7 ga watan Maris na 2020 a Abuja, nan da nan 'yan uwa da abokan arziki suka fara yadawa a kafafen sada zumuntar zamani.
A cewar shugaban matasan jam'iyyar APC din, Qur'ani ne ya bashi damar auren mata 2, 3 ko kuma 4 kuma yayi adalci a tsakaninsu.
Daya daga cikin matansa, Maryam Mohammed mai shekaru 28 ta kammala karatun digirinta a fannin saye da siyarwa ta bayyana yadda taji a lokacin da ya bayyana mata cewa a rana daya zai aureta da matarsa ta biyu mai shekaru 26, Maimuna Mahmoud wacce ta kammala karatunta a fannin tattali.
A cewar matan nasa, da amincewarsu Adamu ya auresu a rana daya saboda soyayya da kuma yadda addini ya tanadar.
Adamu ya shawarci maza da su auri mata biyu don kawar da matsalar soyayya da wata matar a waje.
KU KARANTA: Mun shirya yin sasanci da ƴan bindigan da suka sace ƴaƴanmu, Iyayen ɗaliɓan Kaduna
A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta bataliya ta 192 dake karamar hukumar Gwoza a jihar Borno sun samu nasarar kashe a kalla wasu 'yan ta'adda 12 da ake zargin 'yan Boko Haram ne, jaridar The Cable ta ruwaito.
Da tsakar daren Lahadi ne 'yan ta'addan suka kaiwa sansanin sojojin farmaki. Majiyoyi da dama sun sanar da The Cable cewa sojojin sun yi musayar wuta dasu.
"Rundunar Tango 9 sun yi gaggawar mayar da harin da 'yan ta'adda suka kai musu har suka kashe mutane 7 take yanke, hakan yasa suka ja da baya," Kamar yadda majiyar ta tabbatar.
Asali: Legit.ng