Bidiyo: Wani Mutum Ya Yo Odar Gida Daga China, Ya Dasa Shi A Kan Filinsa

Bidiyo: Wani Mutum Ya Yo Odar Gida Daga China, Ya Dasa Shi A Kan Filinsa

  • Wani matashi mai suna Zackary South a dandalin TikTok ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya da gidansa na kwantena
  • Zackary ya bayyana cewa ya dauke shi tsawon watanni uku kafin ya samu gidan bayan ya yi oda daga kasar China
  • Mutane da dama da suka ga yadda aka hada gidan sun tambayi nawa ya kashe wajen gina gidan

Wani mutum mai suna Zackary South, ya nunawa mutane hanyar da zasu bi wajen mallakar gida sukutum ba tare da amfani da bulo ko siminta ba.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a TikTok, Zackary ya bayyana cewa ya shigo da wani gidan kwantena daga kasar China kuma ya yi odar gidan ne tsawon watanni uku kafin suka iso.

Kara karanta wannan

Kara Tsawo Nake Duk Bayan Wata 3 Ko 4: Wani Dogon Mutum Ya Ba Da Tarihinsa A Wani Bidiyo

Gidan kwantena
Bidiyo: Wani Mutum Ya Yo Odar Gida Daga China, Ya Dasa Shi A Kan Filinsa Hoto: TikTok/@zackarysouth
Asali: UGC

Yadda aka hada gidan

Lokacin da kwantenan ya izo wajensa, sai ya zamana gida ne mai dauka biyu da madafi da kuma bandaki bayan an hada shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Domin hada gidan, sai da iyalin gaba daya suka hadu suka hada hannu yayin da suka yi amfani da abun daga mota wajen daura gidan kan wasu bulo.

Sun bubbude wuraren da aka nade a jikin gidan. Bayan shafe yan awanni sai ga gidan ya kammalu tsaf.

A wani bidiyon, mutumin ya bayyana abun da ya kashe don amsa tambayoyin masu neman sanin nawa ake siyar da gidan. Yace ya biya 20,000 AUD (N5,811,773.59) na ginin sannan 5,000 AUD (N1,452,943.40) kudin kawowa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Steve ya ce:

“Hadadden gida (nawa ake siyarwa) zai yi amfani ga matasa da ke son mallakar gidansu na farko.

Kara karanta wannan

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

Evan Payne795 ya ce:

“Me yasa mutane suka nuna sha’awarsu sosai a kan wannan abun tirela sunansa tirela.”

JOY MARY AMEDA ta ce:

“Nawa ake siyarwa, don zan so mallakar daya.

dontrunfrm45 ya ce:

“Kawai ina son sanin nawa ake siyarwa.”

Gidan Duniya: Wata Budurwa Ta Yada Bidiyon Aljannar Duniyar Da Mahaifinta Ya Gina Musu

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya domin yada bidiyon katafaren gidan da mahaifinta ya gina masu, wurin har yayi masu girma.

A bidiyon, budurwar ta shiga madafi don nuna famfon da ke fitar da ruwan sanyi da na zafi sannan ta hasko falo daban-daban har guda takwas a cikin gidan.

Da take nuno manyan hotuna masu 'dan karen kyau, ta yi barkwanci cewa ta kusa fara siyar da wasu daga cikinsu saboda sun cike ko ina na gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel