Harin yan daba: An tsaurara matakan tsaro yayinda Sufeto Janar na yan sanda zai ziyarci Imo

Harin yan daba: An tsaurara matakan tsaro yayinda Sufeto Janar na yan sanda zai ziyarci Imo

- Sufeto janar na ‘yan sanda na shirin ziyartar Owerri, babban birnin jihar Imo

- Wannan ya biyo bayan harin da aka kaiwa hedikwatar rundunar ‘yan sanda a jihar

- Ku tuna cewa wasu gungun mutane da suka kai hari kan wuraren gyara hali sun saki fursunoni da yawa

Jami’an tsaro sun mamaye unguwannin Owerri, babbar birnin jihar Imo a shirye-shiryen zuwan Sufeto Janar na yan sanda, Muhammad Adamu, jaridar Punch ta ruwaito.

Ziyarar IGP din ya biyo bayan hare-haren safiyar Litinin a kan hedkwatar rundunar yan sanda na jihar a Owerri da kuma cibiyar gyara hali na Owerri.

KU KARANTA KUMA: Buni yana maimaita irin kuskuren Oshiomhole - Kungiyar gwamnonin APC

Harin yan daba: An tsaurara matakan tsaro yayinda Sufeto Janar na yan sanda ya isa Imo
Harin yan daba: An tsaurara matakan tsaro yayinda Sufeto Janar na yan sanda ya isa Imo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yan bindigar da suka saki fursunoni 1,884 sun fada masu cewa “ku je gida, Yesu ya tashi. Babu dalilin da zai sa ku sake kasancewa a nan.”

Sun kuma kona akalla ababen hawa 50 bayan sun saki kusan dukkanin masu laifi a hedkwatar rundunar yan sandan.

Yan bindigar sun kuma kona wani soja a cikin wata mota bayan sun kai hari sansanin sojoji a Ukwuorji a hanyar babban titin Owerri-Onitsha, inda suka kona motocin aikin soji hudu.

An tattaro cewa idan ya isa jihar, IGP zai duba hukumomin yan sandan da aka kaiwa hari.

Kakakin yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu ya tabbatar da ziyarar da IGP zai kai jihar.

A gefe guda, Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Sojojin saman Najeriya (NAF) za su fatattaki ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a Najeriya nan da dan kankanin lokaci.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da yin garkuwa da kawunsa

Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin bikin cin abincin Easter tare da ma’aikatan agajin gaggawa na 013 a Minna, inda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma abokan aikin matukan jirgi uku da suka rasa rayukansu a wani atisaye a ranar 1 ga Afrilu 2021.

Air Marshal Amao ya sake nanata sadaukarwar shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar sojin saman Najeriya don tabbatar da cewa an kawo karshen ta’addanci da ‘yan fashi da makami, Channels TV ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel