'Yan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da yin garkuwa da kawunsa

'Yan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da yin garkuwa da kawunsa

- 'Yan sanda a jihar Kano sun gurfanar da wani mai suna Abubakar Musa wanda yayi garkuwa da kawunsa sannan ya karbi kudin fansa miliyan daya

- An kuma kama wanda ake zargin dauke da bindigogin AK 47 guda biyu

- Ana zargin yana daya daga cikin 'yan fashin da ke gudanar da ayyukansu a Kano, Birnin Gwari a jihar Kaduna da wasu jihohin arewa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 27, Abubukar Musa, wanda suka ce ya sace kawunsa a kan kudin fansar naira miliyan daya.

Kakakin rundunar 'yan sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa, ya aika da wani bidiyo da ke nuna wanda ake zargin a gaban' yan jaridar a ranar Lahadi.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne da bindigogin AK 47 guda biyu da ake zargin ya yi amfani da su wajen aikata laifi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

'Yan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da yin garkuwa da kawunsa
'Yan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da yin garkuwa da kawunsa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun dauki kwakwaran mataki a yayinda fastocin ‘Buhari-Must-Go’ ya bayyana a jihar Arewa

Mista Kiyawa ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana daya daga cikin 'yan fashin da ke gudanar da ayyukansu a Kano, Birnin Gwari a jihar Kaduna da wasu jihohin arewa.

Mista Musa, dan asalin kauyen Rurum da ke karamar hukumar Tudun Wada a Kano, ya ba da labarin yadda ya sace kawun nasa ya kuma karbi kudin fansa kafin ya sake shi a cikin bidiyon.

Wanda ake zargin ya ce ya ari bindigogin da aka samu a hannun sa ne daga Muhammadu Bakanoma da ke jihar Zamfara don tunkarar wani dan fashi da ya kira Malam a Birnin Gwari, wanda ya zarge shi da sace mata da ‘yar sa.

“Ni barawon shanu ne. Na taba yin garkuwa da kawuna Alhaji Haruna da dan baffana Bappan Jauro shekaru shida da suka gabata. Wadannan su ne mutum biyu da na taba sacewa. Na sace shi ne (Alhaji Haruna) saboda yaransa biyu (Medi da Bappan Jauro) sun sace kanwata, Hafsat.

“Na sake shi bayan karbar kudin fansa naira miliyan daya. Yanzu muna zaune tare da shi (Alhaji Haruna) a gida daya,” in ji Mista Musa.

KU KARANTA KUMA: Wani Inyamuri ne ya damfare ni kudi N450 miliyan shiyasa nayi barazanar kashe kaina - Ummi Zeezee

Mista Kiyawa ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike akan lamarin da ake zargin mai laifin da aikatawa.

A wani labarin, rundunar yan sandan ƙasar nan reshen jihar Adamawa ta kama wani ɗan shekara 30 da zargin kashe wani dattijo ɗan shekara 57 a duniya.

Matashin ya kashe dattijon ne saboda yana zargin cewa yana da wata boyayyar alaƙa da matarsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wanda aka kama ɗin mai suna, John Samuel, mazaunin ƙauyen Bandasarga ƙaramar hukumar Ganye, a jawabin yan sanda, ya dawo gida da misalin ƙarfe 11:00 na dare sai ya haɗu da dattijon a cikin gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel