Boko Haram: Babban hafsan sojin sama ya bayyana lokacin da ta'addanci zai zo karshe a Najeriya
- Shugaban hafsan sojin sama ya ba da tabbacin cewa dakarun NAF za su fatattaki ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a Najeriya nan kusa
- Air Marshal Oladayo Amao da Shugaba Buhari da rundunar sojin kasar sun sadaukar da kansu don tabbatar da cewa an kawo karshen ta’addanci da ‘yan fashi da makami
- Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da kokarin dawo da jirgin NAF Alpha Jet Aircraft da ya fadi a ranar 31 ga Maris 2021
Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Sojojin saman Najeriya (NAF) za su fatattaki ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a Najeriya nan da dan kankanin lokaci.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin bikin cin abincin Easter tare da ma’aikatan agajin gaggawa na 013 a Minna, inda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma abokan aikin matukan jirgi uku da suka rasa rayukansu a wani atisaye a ranar 1 ga Afrilu 2021.
KU KARANTA KUMA: Buni yana maimaita irin kuskuren Oshiomhole - Kungiyar gwamnonin APC
Air Marshal Amao ya sake nanata sadaukarwar shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar sojin saman Najeriya don tabbatar da cewa an kawo karshen ta’addanci da ‘yan fashi da makami, Channels TV ta ruwaito.
Babban hafsan sojin saman wanda ya samu wakilcin Air Vice-Marshal Remiqius Ekeh ya yaba wa rundunar ta 013 da ke ba da agajin gaggawa da kuma bangaren rundunar na GAMA AIKI tare da hafsoshi, da su ci gaba da jajircewa wajen yaki da ta’addanci.
Ya gaya musu cewa kada su gaji wajen sadaukar da kansu da kuma aiki tukuru don cimma nasarar kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
Shugaban NAF din ya bayyana cewa ana ci gaba da kokarin dawo da jirgin NAF Alpha Jet Aircraft da ya fadi a ranar 31 ga Maris 2021.
A cewarsa, ikirarin cewa mahara ne suka harbo jirgin karya ne.
KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun dauki kwakwaran mataki a yayinda fastocin ‘Buhari-Must-Go’ ya bayyana a jihar Arewa
Ya yi alkawarin cewa za a bayyana hujjojin da ke akwai lokacin da bincike ya kammala.
A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kira yi matasa da su farka daga barcin da suke don kare kasar nan daga tarwatsewa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewar gwamnan, wannan shine lokacin da yafi dacewa matasa su tsunduma harkar siyasa don su kasance cikin masu yanke hukunci a cikin dukkan matakan siyasa na ƙasar nan.
Matawalle ya faɗi haka ne a Kaduna ranar Litinin, jim kaɗan bayan an bashi kyautar 'Abin koyin matasa da ɗalibai' wanda ƙungiyar matasa da ɗaliban arewa ta bashi.
Asali: Legit.ng