Ku fito ku ceci Najeriya daga tarwatsewa, Gwamnan Zamfara ya roƙi Matasa

Ku fito ku ceci Najeriya daga tarwatsewa, Gwamnan Zamfara ya roƙi Matasa

- Gwamnan Zamfara, Bello matawalle ya roƙi matasan ƙasar nan da su fito a dama da su a dukkan muƙaman siyasar ƙasar nan

- A bayanin gwamnan ya ce matasa sune ƙashin bayan al'umma, don haka wannan shine lokacin da ya dace su fito a dama da su

- Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wani taro a Kaduna, inda aka bashi lambar yabo ta 'Abin koyi ga matasa da Ɗalibai' wanda ƙungiyar matasa da ɗaliban arewa ta bashi

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kira yi matasa da su farka daga barcin da suke don kare kasar nan daga tarwatsewa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwamna El-Rufai zai hukunta duk wanda ya yi sulhu da ‘Yan bindiga a jihar Kaduna

A cewar gwamnan, wannan shine lokacin da yafi dacewa matasa su tsunduma harkar siyasa don su kasance cikin masu yanke hukunci a cikin dukkan matakan siyasa na ƙasar nan.

Matawalle ya faɗi haka ne a Kaduna ranar Litinin, jim kaɗan bayan an bashi kyautar 'Abin koyin matasa da ɗalibai' wanda ƙungiyar matasa da ɗaliban arewa ta bashi.

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Gusau da Tsafe a majalisar tarayya, Kabir Amadu Mai Palace, shi ne ya wakilci gwamnan a wajen taron.

Ku fito ku ceci Najeriya daga tarwatsewa, Gwamnan Zamfara ya roƙi Matasa
Ku fito ku ceci Najeriya daga tarwatsewa, Gwamnan Zamfara ya roƙi Matasa Hoto: @Bellomatawalle1
Source: Twitter

A jawabinsa ya ce:

"Ni matashi ne kamar ku, wannan shine lokacin da yafi dacewa mu shiga siyasa. Bamu da dalilin ƙin yin hakan, domin ƙasar mu na gab da tarwatsewa kuma mune kaɗai hanyar da za'a bi wajen ceto ƙasar."

"Akwai buƙatar matasa su shiga harkar siyasa sosai-sosai. Idan muka duba yawan al'ummar ƙasar nan, matasa sune suka fi yawa. Saboda haka lokaci ya yi da matasa zasu fito su shiga gwamnati ko don su ceci ƙasar nan."

KARANTA ANAN: Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno

"A siyasar Najeriya, da zaran kace matashi ya fito ai takara da shi a siyasa, tambayar da zai fara yi maka shine ina zai sami kuɗin da zai yi hakan. Abinda yakamata matasa su gane, ana buƙatar su a jam'iyyar siyasa."

Ya ƙara da cewa, kamar yadda na saba faɗa, wani lokacin ƙalubalen da matasa ke fuskanta shine su da kansu. Inda matasa zasu haɗa kansu waje ɗaya da yawan kuri'un da suke dashi, to zasu iya ƙwace mulki tun daga shugaban ƙasa har zuwa kansila.

Gwamnan ya ƙara da cewa, idan kuka duba tun daga ranar da muka shiga ofis, gwamnatin jihar Zamfara ta matuƙar maida hankali wajen kyautata fannin ilimi da kuma samar ma matasa aikin yi.

A cewarsa su matasa sune ƙashin bayan al'umma, kuma sune shuwagabannin gobe, don haka ya zama wajibi a kula da su dan samun kyakkyawan gobe.

A Wani labarin kuma 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

Sanawar da rundunar ta fitar ya ce jami'an Puff Adder II ne suka kashe shi a kauyen Tsibiri kusa da dajin Sububu.

Yan sandan sun kuma yi artabu da wasu yan bindigan inda suka kashe guda suka kwato makamai da layyu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel