'Yan sanda sun dauki kwakwaran mataki a yayinda fastocin ‘Buhari-Must-Go’ ya bayyana a jihar Arewa

'Yan sanda sun dauki kwakwaran mataki a yayinda fastocin ‘Buhari-Must-Go’ ya bayyana a jihar Arewa

- Yan sanda sun damke wasu mutane biyu da ke lika fastocin adawa da Buhari a jihar Kogi

- ‘Yan sanda sun ce ayyukan mutanen biyu ba za a kira shi a matsayin zanga-zangar lumana ba

- Da take martani a kan ci gaban, gwamnatin jihar Kogi ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci siyasar raba kai daga kowani mutum ba

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi ta cafke wasu mutane biyu da ba a bayyana sunayensu ba da ake zargi da shirin fara kamfen din bata sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a Lokoja, babban birnin jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kwamishinan yan sanda na jihar Kogi, Ayuba Edeh, ya tabbatar da kamun a ranar Litinin, 5 ga watan Afrilu.

Legit.ng ta tattaro cewa an kama mutanen biyu da misalin karfe 2:30 na tsakar dare yayin da suke zana gine-gine da lika fastoci dauke da rubutun: 'Dole ne Buhari ya tafi'.

'Yan sanda sun dauki kwakwaran mataki a yayinda fastocin ‘Buhari-Must-Go’ ya bayyana a jihar Arewa
'Yan sanda sun dauki kwakwaran mataki a yayinda fastocin ‘Buhari-Must-Go’ ya bayyana a jihar Arewa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Edeh ya bayyana cewa yayin da ‘yan kasa ke da‘ yancin yin zanga-zanga, dole ne a yi hakan ta hanyar da ta dace ba tare da tunzura jama’a ba, Daily Trust ta kuma ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Wani Inyamuri ne ya damfare ni kudi N450 miliyan shiyasa nayi barazanar kashe kaina - Ummi Zeezee

Shugaban 'yan sandan ya kara da cewa da samarin ba za su yi zanga-zanga cikin dare ba, yana mai cewa ba za a iya kiran zanen bango da manna fastocin adawa da Buhari a matsayin zanga-zangar lumana ba.

Gwamnatin Kogi ta mayar da martani

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya yaba wa matasan, yana mai cewa su ne suka cafke masu zanga-zangar kin jinin Buhari suka mika su ga ‘yan sanda.

Fanwo ya ce jihar Kogi ta kasance matattarar shugaba Buhari mai karfi, yana mai zargin cewa an bugo fastocin adawa da Buharin ne a jihar kudu maso kudu.

Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen inganta rayuwar mutane kuma ba za ta yarda kowa ya yi siyasar raba kawunan jama'a ba.

KU KARANTA KUMA: Wani Mutumi ya kashe ɗan shekara 57 saboda zargin yana da ɓoyayyar Alaƙa da Matarsa

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shekaru bakwai kenan da kafa jam'iyyar APC amma har yanzin ba ta zama haɗaɗɗiyar jam'iyya ba.

Gwamnan ya bayyana jam'iyyar da cuɗuwar jam'iyyun siyasa da suke faman ganin sun zama jam'iyya ɗaya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Ganduje ya yi wannan jawabi ne a wani taro da kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin APC na yankin arewa maso yamma ya shirya a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel