Wani Inyamuri ne ya damfare ni kudi N450 miliyan shiyasa nayi barazanar kashe kaina - Ummi Zeezee

Wani Inyamuri ne ya damfare ni kudi N450 miliyan shiyasa nayi barazanar kashe kaina - Ummi Zeezee

- Tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim ta bayyana dalilin da yasa tace tana son kashe kanta

- Ummi Zeezee ta ce wani abokin kasuwancinta ne ya damfare ta kudi har naira miliyan 450 wanda hakan ne ya jefa ta a cikin kuncin rayuwa

- Ta ce sun tattauna da mutumin da nufin cewa zai saka ta a harkar siyar da danyen mai

Tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Ummi Ibrahim wacce aka fi sani da Ummi Zeezee ta bayyana dalilinta na barazanar kashe kanta.

A hira da muryar Amurka tayi da Zeezee, tace tayi wannan yunkuri ne sakamakon damfararta da wani Inyamuri yayi.

A cewarta, Inyamurin ya nemi suyi harkar danyen mai inda ta zuba kudin da ya kai naira miliyan 450.

Wani Inyamuri ne ya damfare ni kudi N450 miliyan shiyasa nayi barazanar kashe kaina - Ummi Zeezee
Wani Inyamuri ne ya damfare ni kudi N450 miliyan shiyasa nayi barazanar kashe kaina - Ummi Zeezee Hoto: ummizeezee
Asali: Instagram

KU KARANTA KUMA: Bishop Kukah ya saki zazzafan sakon bikin Ista, ya sake caccaka Buhari

Ta ce:

“Dalilin da yasa naji kamar na kashe kaina shine akwai wani inyamuri, dan Neja Delta ne sai muka yi kasuwanci da shi irin na abin da ya shafi danyen mai.

"Sai muka zauna muka tattauna a kan wannan kasuwanci cewa Ina so in shiga, sai ya yanke mun wasu kudi yace da shi zan fara kasuwancin idan ya so idan kasuwancin yayi karfi na ga na ci riba sai na cika masa sauran kudin.Ashe kawai irin dan damfarar nan ne.

“Sai da na ba da kudi kuma makudan kudade ne na tura masa. A dala na bashi amma idan aka mayar da shi naira ya kai kimanin N450 miliyan.

"Da na bashi ashe ya damfare ni ne. Kawai yana tafiya a kan wannan satin ne zai dawo, idan ya dawo Za mu tattauna sai ya bani riba tunda na riga da na ba da kudaden. Wani abun mamaki harda Turawa ya zo nan, don haka dole ne na saki jiki cewa wannan kasuwancin gaskiya ne.

“Na san shi ne a Lagas tunda a chan na fi zama. Mun taba kasuwanci da shi kuma na ci riba sai nake ganin ba zai cuceni ba. Kawai sai na nemi wayansa ban samu ba. Na duba shafukan sa na soshiyal midiya sai naga ya toshe ni.

Sai dai ta ce ba duka kudaden da ta tara ya damfare ta ba tana mai cewa:

“Ba duka kudaden da na tara bane, amma koda mutum Gwamna ne yayi asarar wannan kudade sai ya jijjiga balantana ni yar kasuwa."

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kubutar da dalibai 5 daga cikin 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

Kan sana’ar da take yi har ta tara wannan kudaden ta ce:

“Sana’o’in da nake yi manyan gwamnoni na bani kwangila. Kuma wannan sana’ar da aka damfareni na harkar mai Ina yin shi. Ina saro tankokin sannan ina siyarwa manyan iyayen gidana.

“Ina kwangilar gyaran titi, asibitoci, makarantu, kasuwancin da nake yi kenan Ina samun kudi. Wannan ne ya sa na ji kamar na kashe kaina saboda yayi mun rugu-rugu.

"Ban kai kara ba kawai na ba kaina sati daya ne kwakwalwata ta huta sannan na san ta inda zan billo.”

A baya mun ji cea Ummi Zeezee, ta ce ta shiga kangin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.

A ranar Asabar, 3 ga watan Afrilu ne jarumar ta fadi hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Sai dai jarumar wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu ”Jinsi,” “Gambiza” da "Tutar So" ta ce kada kowa ya tambaye ta dalilin da ya sa take so ta aikata wannan danyen aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel