Bishop Kukah ya saki zazzafan sakon bikin Ista, ya sake caccaka Buhari

Bishop Kukah ya saki zazzafan sakon bikin Ista, ya sake caccaka Buhari

- Gwamnati mai ci karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta sha fuskantar hare-hare kan yadda ta ke tafiyar da matsalolin tsaronNajeriya

- Da yake waiwayar halin da Najeriya da ‘yan kasar ke ciki a yanzu, Kukah, mai sukar lamarin gwamnati mai ci, ya ce matsalolin kasar na karuwa a kulla-yaumin

- A cikin sabon sukar da ya gabatar a sakon sa na Ista, Kukah ya zargi wadanda ke kan mulki kan karuwar lamura na 'yan fashi da sauran laifuka

A yayin da mabiya addinin kirista a duniya ke bikin Ista, Limamin cocin Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya yi amfani da damar wajen sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A sakon nasa na Ista na 2021 mai taken, ‘Kafin daukakarmu ta tashi’, malamin ya ce masu tayar da kayar baya suna cin karensu babu babbaka a karkashin kulawar Buhari, Channels TV ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ku tayani da addu'a, ina cikin kangin rayuwa har ina ji kamar na kashe kaina, Ummi Zeezee

Bishop Kukah ya saki zazzafan sakon bikin Ista, ya sake caccaka Buhari
Bishop Kukah ya saki zazzafan sakon bikin Ista, ya sake caccaka Buhari Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Kukah ya tuna cewa Buhari ya bayyana kungiyar Boko Haram a matsayin wani yanayi na kananan gobara da ke haifar da babban gobara a yayin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a 2015.

Ya ce:

“Yanzu, a karkashin kulawarsa, gobarar tana cin al’ummar, kuma a lokuta da yawa, hakika suna fara da kaɗan- kaɗan.

"Gaba daya, matsalolin Najeriya na ci gaba da girma a kulla-yaumin, amma dole ne hannayenmu su ci gaba da mikewa cikin addu'a."

’Yan Najeriya na cikin wani hali

Premium Times ta ruwaito cewa bishop din na Katolika ya ce abin da Najeriya ke ciki a halin yanzu shi ne tunatar da halin da Isra’ila ke ciki wanda ya kai ga mutuwar Eli, wanda ya kasance babban malami.

Ya lissafa wasu daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu, wadanda suka hada da rikicin Boko Haram, fashi da makami, satar mutane da sauran muggan laifuka. A cewarsa, wadannan suna haifar da tsoro kan ko "daukakar Najeriya na gab da gushewa".

KU KARANTA KUMA: Mutane da dama za su iya yin umrah lokacin Ramadan, Saudiyya

Ya ce 'yan fashi suna ta yin dirar mikiya, suna azabtar da' yan kasar da suka tagayyara a kowace rana.

A wani labarin, Ndinne Igbo, wata kungiyar zamantakewar mata, ta yi barazanar cewa mambobinta za su yi tattaki tsirara a fadin kasar ta Igbo don nuna rashin amincewa da kashe-kashen da makiyaya ke yi a yankin idan har hukumomin da abin ya shafa ba su shawo kan lamarin ba.

Yankin kudu maso gabas na fama da rikice-rikicen makiyaya a makwannin da suka gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da harin makiyaya da ya auku a jihohin Enugu da Ebonyi, inda ta koka kan yadda yara ‘yan kabilar Ibo da dama suka zama cikin mummunan harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel