Yadda 'yan Biafra masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo

Yadda 'yan Biafra masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo

- Rahotannisun bayyana kisan al'ummar Hausa a wani yankin jihar Imo da 'yan Biafra suka yi

- Sun hallaka Hausawa sama da 12, yayin da suka barnatar da dukiyar da ta haura mNaira miliyan 40

- Shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa, da sanin hukumomin tsaro hakan ke faruwa a yankin

Rahotanni daga jihar Imo sun bayyana cewa mutum uku sun hallaka bayan wani hari da ake zargin Kungiyar mayakan Biafra ta kai wa al'ummar Hausawa da ke yankin Orlu a jihar ta Imo.

Lamarin dai ya jefa al'ummar Hausawan da ke yankin cikin zaman zulumi.

A cewar wani dan kasuwa Bahaushe mazaunin yankin na Orlu, Alhaji Amadu Ali, tun daga watan Agustan bara zuwa yanzu, kungiyar ta Biafra ta halaka Hausawa 12 baya ga asarar dukiya da suka tafka da haura ta kusan naira miliyan 42.

"Mu dai mun tashi kawai ranar Laraba, wani mai nama, yana tafiya ya dawo da wuri kawai ya haɗu da wadannan mutanen suka bude masa wuta, suka sakar masa harsashi na AK47, nan take ya mutu", in ji Alhaji Ahmadu Ali.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP za ta ba matan Abuja fom din tsayawa takara kyauta

Yadda masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo
Yadda masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo Hoto: dailypost.ng
Source: UGC

Ya fadawa BBC cewa lamarin ba mai naman kadai ya shafa ba har da wani dan sarkin gari da shi ma yake sayar da nama wanda suka halaka shi.

Dan kasuwar ya ce ba zai iya bayanin wani dalili da ya sa tsagerun na Biafran suke kai musu hari ba "don bama fada da kowa, ba ma tsakonar kowa".

"Tun daga ranar da aka yi (rikicin) Endsars suka fara kashe mutanenmu daya bayan daya", in ji Alhaji Amadu Ali.

Ya ce kawo yanzu, yan Biafran ba su fara bin gida-gida ba amma suna kai hari ne kan masana'antun Hausawa inda suke harbe su da bindiga.

Ya yi ikirarin cewa hukuma tana sane da abin da ke faruwa a jihar saboda "'yan sanda su suka bamu motar da muka dauki gawar mutum uku muka binne kuma sai da kwamishinan 'yan sanda ya yi magana a bamu gawar sannan aka bamu".

KU KARANTA: Wasu mutum 7 sun sheka lahira bayan yi allurar rigakafin Korona a Burtaniya

A wani labarin daban, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce fitattun mutane ne ke ingiza Najeriya zuwa ga wargajewa, The Cable ta ruwaito.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar, Lawan ya ce talakawa na ganin cewa ya kamata kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayin dunkulalliya da ta fi karfin ballewa.

"Na yi imanin cewa yawancin 'yan Najeriya sun yi imanin ya kamata su kasance a inuwa daya - ina nufin talakawan Najeriya," in ji Lawan a garinsu, jihar Yobe.

“Wadannan mutane ne da suka yi imani da hadin kan kasar nan. Amma fitattu nan ne inda matsalar take.

Source: Legit

Online view pixel