Sakon Osinbajo ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, abubuwa za su daidaita
- Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya tura sakon bikin Ista zuwa ga dukkan 'yan Najeriya
- Osinbajo ya bukaci 'yan Najeriya da su sa rai a rahamar Allah cewa kasar za ta daidaita
- Ya kuma yi addu'ar fatan 'yan Najeriya su dandana rahama da jinkan ubangiji saboda Ista
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, SAN, a ranar Lahadi, ya karfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwa da cewa “su yi babban fatan cewa abubuwa za su daidaita a kasar nan ”. Daily Trust ta ruwaito.
Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai bayan kammala bikin Ista a ranar Lahadi a Aso Villa Chapel.
A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan yada labarai da, Laolu Akande, Osinbajo ya yi addu'ar cewa Najeriya za ta dandana alheri da rahamar Allah.
KU KARANTA: Sheikh Gumi da Obasanjo sun shawarci gwamnati da ta kirkiri kotun 'yan bindiga
Jawabin an yi masa taken, ‘Sakon Ista na Osinbajo ga 'yan Najeriya: Komai zai daidaita a Kasarmu ’.
“Ina so in gode wa Allah saboda kasarmu, kuma in yi addu’a cewa al’ummarmu za su dandana alheri da rahamar Allah ta hanyoyi daban-daban da muke tsammanin alherinsa da jinkansa.
"Komai zai yi kyau cikin sunan Yesu," Akande ya ruwaito mataimakin shugaban na cewa.
Yayin da yake yiwa 'yan Najeriya murnar bikin Ista, Osinbajo ya kara da cewa sakon Ista sako ne na musamman kuma mafi girman kauna da alherin Allah.
Osinbajo ya ci gaba da cewa lokacin Ista ya kasance “babban abin farin ciki saboda muna murna da shaida tsarin Allah. Ta wata hanya kuwa, Allah ya bamu tikitin ceton kanmu kuma hakan abin farin ciki ne kwarai da gaske."
KU KARANTA: Yanzun-yanzu: Kasar Indiya ta ba Najeriya gudunmawar rigakafin Korona 100,000
A wani labarin daban, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce fitattun mutane ne ke ingiza Najeriya zuwa ga wargajewa, The Cable ta ruwaito.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar, Lawan ya ce talakawa na ganin cewa ya kamata kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayin dunkulalliya da ta fi karfin ballewa.
"Na yi imanin cewa yawancin 'yan Najeriya sun yi imanin ya kamata su kasance a inuwa daya - ina nufin talakawan Najeriya," in ji Lawan a garinsu, jihar Yobe.
Asali: Legit.ng