Obasanjo ya bi sahun Gumi, ya roki gwamnatin Buhari ta yafewa tubabbun 'yan bindiga

Obasanjo ya bi sahun Gumi, ya roki gwamnatin Buhari ta yafewa tubabbun 'yan bindiga

- Tsohon shugaban kasan Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Sheikh Gumi kan batun yafewa 'yan bindiga

- Ya shawarci gwamnatin Buhari ta yi afuwa ga tubabbun 'yan bindiga da suka shirya barin daji

- Wannan ne karo na farko da Obasanjo ya yi irin wannan batu kan matsalar tsaro dake damun kasar

Tsohon shugaban kasa Obasanjo da Fitaccen Malamin addinin Islama a Arewacin Najeriya, Sheikh Ahmed Gumi sun nemi gwamnatin Buhari ta yi wa tubabbun 'yan bingida afuwa, BBC ta ruwato.

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa ta sirri da Malamin addinin da tsohon shugaban Najeriyan suka yi a gidansa da ke jihar Ogun a jiya Lahadi 4 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Sakon Osinbajo ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, abubuwa za su daidaita

Obasanjo ya bi sahun Gumi, ya roki gwamnatin Buhari ta yafewa tubabbun 'yan bindiga
Obasanjo ya bi sahun Gumi, ya roki gwamnatin Buhari ta yafewa tubabbun 'yan bindiga Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Obasanjo ya ce, "Yan bindigar da suka shirya fita daga daji da kuma daina muggan laifuka, a yi musu afuwa a gyara halayyarsu a koya musu ayyuka a basu jari ya zama suna da aikin yi".

Wannan ne karon farko da aka ji tsohon shugaban na furta irin wadannan kalamai dangane da matsalar rashin tsaro dake addabar Arewa kuma ake hasashen ta kusa mamaye yankuna da yawa a kasar Najeriya.

Sai dai kuma ba wannan ne karon farko ba da Sheikh Gumi ke neman a yi wa 'yan bindigar afuwa ba.

Sheikh Gumi ya shahara wajen shiga daji tare da tattaunawa da 'yan bindiga don shawo kan matsalar rashin tsaro a yankunan Arewa.

Lamarin ganawar Gumi da shugabannin 'yan bindiga ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya wanda ya jawo wasu ke ganin Gumi ya zama mai magana da yawun 'yan bindiga.

KU KARANTA: Yanzun-yanzu: Kasar Indiya ta ba Najeriya gudunmawar rigakafin Korona 100,000

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wani fitaccen malamin addini a Arewa, Sheikh Ahmad Gumi, sun ba da shawarar kafa kotuna na musamman da za su yi shari’ar ’yan bindiga, masu satar mutane da masu safarar muggan makamai a Najeriya.

Obasanjo da Gumi sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka sanya hannu bayan sun yi wata ganawar sirri a dakin karatun Obasanjo dake Abeokuta a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

A wani bagnaren sanarwar, ance; “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki batun da muhimmanci a tsakanin ECOWAS don yin aiki a magance matsalar yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.