EFCC za ta binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi karfinsu a shafukan sada zumunta

EFCC za ta binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi karfinsu a shafukan sada zumunta

-EFCC da ICPC za su binciki dukkan 'yan Najeriya masu nuna dukiya a kafafen sada zumunta

- Wannan ya biyo bayan umarnin da shugaban EFCC ya bayar na bincikar ma'aikatan banki

- An bayyana cewa, yanzu zai zama doka a Najeriya cewa, za a iya bincikar dukiyar 'yan kasa

Mataimakiya ga shugaban kasar Najeriya kan kafofin sada zumunta, Laurette Onochie, ta ce hukumomin da ke yakar cin hanci da rashawa wato EFCC da ICPC za su binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsu musamman a shafukan sada zumunta.

Ms Onochie ta shaida hakan ne a shafinta na Twitter ranar Litinin, tana mai cewa za a gayyaci irin wadanan mutane domin bincike kan yaddaa suka mallaki kadarori da arzikin da suke shelantawa.

KU KARANTA: Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba

EFCC za ta binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi karfinsu a shafukan sada zumunta
EFCC za ta binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi karfinsu a shafukan sada zumunta Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Onochie ta ce, "binciken yadda mutum ya ke rayuwarsa za ta kasance wajibi a Najeriya bisa sharuda na doka".

Wannan na zuwa ne bayan a makon da ya gabata, shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya fitar da sanarwa cewa wajibi ne duk wani ma'aikacin banki ya bayyana kadarorin da ya mallaka.

KU KARANTA: Gandollar: Idan wani abu ya same ni, a tuhumi Ganduje, Jaafar Jaafar ga IGP

A wani labarin, Hukumar EFCC a Najeriya ta umarci ma’aikatan banki da su bayyana kadarorinsu da suka mallaka ta kuma bada wa'adi zuwa ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021, The Cable ta ruwaito.

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce sun tattauna kan kokarin da hukumar ke yi na kawar da laifukan kudi a kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel