Rundunar Yan Sanda ta sheƙe yan garkuwa da mutane a wani Batakashi da suka yi

Rundunar Yan Sanda ta sheƙe yan garkuwa da mutane a wani Batakashi da suka yi

- Hukumar yan sanda a jihar Neja ta samu nasarar aika yan biɓdiga uku zuwa lahiya a wani musayar wuta d suka yi tsakaninsu

- A cewar yan sandan, sun sami wannan nasara ne tare da taimakon yan bijilanti da kuma wata masaniya da aka basu

- Kwamishinan yan sandan jihar yace mutane su kwantar da hankalinsu, kuma sukai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi a jikinsa

Rundunar yan sanda reshen jihar Neja ta ce masu garkuwa da mutane uku sun rasa rayukansu a wani bata kashi da suka yi a tsakanin su.

Yan sandan sun sami wannan nasara ne tare da haɗin guiwar jami'an sa kai (Vigilante) na garin Lapai.

KARANTA ANAN: Sheikh Gumi ya jagoranci Malamai sun kaima tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo Ziyara

An kashe mutanen ne bayan samun sahihin bayanai da jami'an yan sanda suka yi cewa wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku a wurare daban-daban.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce jami'ai tare da yan bijilanti sun bi su a baya har zuwa wani daji a ƙauyen Fapo, dake ƙaramar hukumar Lapai.

Inda anan ne jami'an suka far musu akai batakashi tsakanin su, har yan sandan suka samu nasar kashe mutum uku.

Rundunar Yan Sanda ta sheƙe yan garkuwa da mutane a wani Batakashi da suka yi
Rundunar Yan Sanda ta sheƙe yan garkuwa da mutane a wani Batakashi da suka yi Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Wasi'u Abiodun, ya ƙara da cewa sun kuma ƙwato bindigu guda biyu ƙirar AK-47 da kuma wata bindiga ta gargajiya guda ɗaya, Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: NSCDC ta lalata wata Maɓoyar Man Fetur a Delta, Ta Cafke Mutum shida

Ya kuma tabbatar da cewa sauran yan bindigar sun gudu da raunukan harbi a jikin su, sannan kuma an kuɓutar da mutane ukun da suka sace.

Hakanan kuma, kwamishinan 'yan sandan jihar, Adamu Usman, ya yi kiɗa ga al'umma da su kwantar da hankalinsu, jami'ai zasu cigaba da yaƙar duk wani wanda baya buƙatar zaman lafiya.

Ya kuma roƙi mutanen jihar Neja da su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi a jikinsa ga ofishin yan sanda mafi kusa da su.

A wani labarin kuma Duk da umarnin hani daga kotu, masaurautar Kano ta fara yanka filin Idin 'Yar Akwa

Kusan awanni 48 bayan wata Babbar Kotu a jihar Kano ta ba da umarnin hana Masarautar Kano yanka filaye a Filin Sallar Idi na 'Yar Akwa, majalisar masarautar ta ci gaba da yin hakan.

Wata kungoiyar mazauna a yankin ta ci alwashin dakatar da badakalar ta yadda ya dace.

Source: Legit

Online view pixel