NSCDC ta lalata wata Maɓoyar Man Fetur a Delta, Ta Cafke Mutum shida

NSCDC ta lalata wata Maɓoyar Man Fetur a Delta, Ta Cafke Mutum shida

- Hukumar NSCDC ta samu nasarar lalata wata boyayyar matatar man fetur da ake gudanar da ita ba bisa ka'ida ba a jihar Delta

- Hukumar tace ta kama mutane shiga da ake zargi a ya yin samamen da ta kai, kuma ta ce wannan somin taɓi ne, zata kamo duk masu hannu a lamarin

- Sai dai ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya ce ya shiga aikin ne don ya samu kuɗin da zai gudanar da jana'izar mahaifiyarsa da ta mutu.

Hukumar tsaro ta NSCDC ta bayyana cewa ta lalata wata matatar man fetur da ba bisa ƙa'ida ba kuma ta kama mutum shida da ake zargi.

Hukumar ta ce tana zargin mutanen ne da aikin tace man fetur ba bisa ƙa'ida ba a Olokpobiri, Ƙaramar hukumar Warri ta kudu maso yamma, jihar Delta.

KARANATA ANAN: Mutane da dama za su iya yin umrah lokacin Ramadan, Saudiyya

Kwamandan NSCDC na jihar, Mr. Chike Ikpeamonwu, ya bayyana haka a Asaba, babban brninn jihar ranar Asabar, kmar yadda Punch ta ruwaito.

Ya kuma ƙara da cewa waɗanda ake zargin matas ne dake da shekaru tsakanin 18 zuwa shekara 25.

Ikpeamonwu ya ce, tace man fetur ba bisa ƙa'ida ba barazana ce ga tattalin arziƙin ƙasa da kuma lafiyar al'umma, kuma ya ce za su cigaba da ƙoƙari wajen zaƙulo duk wanda ke da hannu a lamarin.

NSCDC ta lalata wata Maɓoyar Man Fetur a Delta, Ta Cafke Mutum shida
NSCDC ta lalata wata Maɓoyar Man Fetur a Delta, Ta Cafke Mutum shida Hoto: @OfficialNSCDC
Asali: Twitter

Ya ce: "Bawai waɗannan ne kaɗai ba, su yaran wani ne kawai. Amma shi babban gwaskan na can wani waje a boye, zamu yi bincike kuma zamu kamo shi."

"Muna fuskantar ƙalubale wajen samun damar usa ga irin waɗannan wurare da ake irin wannan aikin. Amma duk da haka an lalata wasu, wasu kuma suna cigaba da gudanar da aikinsu."

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Kwamishinan jihar Anambra da aka Kama a Harin da aka kaima tsohon gwamna Ya Kuɓuta

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Friday Akokoma, ya ams ƙaifinsa, ya bayyana cewa ya shiga wannan harka ne don ya samu kudin da zai gudanar da janazar mahaifiyarsa.

Ya ce abokinsa ne ya kawo shi ya yi aiki a wurin don ya samu kuɗi ya rufama mahaifiyarsa asiri bayan mutuwarta.

Kwamandan NSCDC ya ce, lalata matatar ta Kanto dake Olokpobiri, ƙaramar hukumar Warri ta kudu maso yamma ɗaya ne daga cikin ƙoƙarin hukumar su na ceto yankin daga lalacewa.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP za ta ba matan Abuja fom din tsayawa takara kyauta

Kwamitin aiki na kasa (NWC) na jam'iyyar PDP ya cire dukkan 'yan takara mata a biyan kudin fom din tsayawa takara a zaben shugabannin kananan hukumomin FCT.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wani jadawalin ayyuka da Austin Akobundu, sakataren shirya taro na kasa ya fitar a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel