Duk da umarnin hani daga kotu, masaurautar Kano ta fara yanka filin Idin 'Yar Akwa
- Biyo bayan umarnin kotu na dakatar da sayar da fili Idin 'Yar Akwa an fara yankan filin
- Mazauna yankin sun wayi gari sun ga 'yan sanda da ma'aikatan yankan fili na aiki a ciki
- Wata kungoiyar mazauna a yankin ta ci alwashin dakatar da badakalar ta yadda ya dace
Kusan awanni 48 bayan wata Babbar Kotu a jihar Kano ta ba da umarnin hana Masarautar Kano yanka filaye a Filin Sallar Idi na 'Yar Akwa, majalisar masarautar ta ci gaba da yin hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake jawabi ga manema labarai a farfajiyar filin ranar Asabar, shugaban kwamitin filin daga yankin, Tijjani Yahaya, ya ce sun yi mamakin cewa bayan umarnin kotu, sai kawai suka wayi gari da safe suka ga ana aikin yankan filin.
Ya bayyana cewa, ’yan sanda dauke da makamai a cikin motoci kusan biyar suna bai wa wasu mutanen da aka turo don yankan filin kariya.
KU KARANTA: Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura ya gudana a kasar Masar
Ya tunatar cewa filin da ake magana akai marigayi Sarki Ado Bayero ne ya bayar da shi ga mazauna yankin don amfani da shi a matsayin wurin Sallar Idi, wanda daga baya gwamnatin jihar Kano ta sanya shi a filyenta, bayan kirkirar Darmanawa Layout.
A cewarsa, a shekarar 2019, kungiyar ta nemi Ofishin kula da filaye lokacin da suka lura da yunkurin mamaye filin, wanda shi ne kadai filin Idi a duk karamar hukumar Tarauni.
Bayan haka, shugaban ya bayyana cewa kungiyar ta tuntubi mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero game da yunkurin kwace filin da Ado Bayero Royal City Trust Fund ta yi don sauya filin zuwa wuraren zama tare da sayar dashi.
Ya kuma bayyana cewa Sarkin ya nemi bangarorin biyu da su tabbatar da zaman lafiya sannan ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.
Mista Yahaya ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta yi duk abin da doka ta tanada don karewa da hana cin zarafi ba bisa ka’ida ba da kuma dakile yunkurin sayar da filin na Sallar Idi.
Mai magana da yawun sarkin, Ahmad Bayero, bai amsa kira ba da sakon tes da aka nemi masarautar ta amsa kan lamarin.
KU KARANTA: Yadda 'yan Biafra masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo
A wani labarin, Wasu yan jihar Kano karkashin kungiyar cigaban Darmanawa Layout, na zargin asusun lamunin birnin Ado Bayero, wani asusun masarautar Kano, da yunkurin kwace filin Idi da kuma sayar da shi.
Shugaban kwamitin filin Idi, Barista Tijjani Yahaya, ya bayyanawa manema labarai a jihar Kano cewa marigayi Ado Bayero ne ya bayar da filin kyauta ga garin kuma gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan.
Tijjani Yahaya ya bayyana cewa irin haka ya taba faruwa a 2019 lokacin da wasu sukayi kokarin sayar da filin.
Asali: Legit.ng