Sheikh Gumi ya jagoranci Malamai sun kaima tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo Ziyara

Sheikh Gumi ya jagoranci Malamai sun kaima tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo Ziyara

- Shahararren malaminnan, Sheikh Gumi ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da safiyar yau don tattaunawa da shi

- Rahotanni sun tabbatar da zuwan malamin tare da wasu malaman addini kuma a yanzun haka suna tsakar tattaunawa da Obasanjo

- Malam Gumi dai na ganin cewa za'a iya magance matsalar tsaron ƙasar nan ta hanyar tattaunawar sulhu da yan bindiga

Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya kai ziyara ga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, Jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa shahararren malamin na can a yanzu haka sun gudanar da taro da Obasanjo.

KARANTA ANAN: Duk Soki Burutsu ne, Bamu naɗa kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, El-Rufa'i ya maida Martani

An ruwaito cewa malamin ya isa gidan tsohon shugaban ƙasar dake garin Abeokuta da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Lahadi.

Mai taimaka ma Obasanjo kan harkokin yaɗa labari, Kehinde Akinyemi, ya tabbatar da zuwan malamin ga jaridar Dailytrust, ya kuma ce akwai wasu shugabannin addinai da suka halarci taron.

"Eh hakane, yanzun haka Gumi na tare da Baba (Obasanjo) suna tattaunawa tare da wasu shugabannin addinai," inji Akinyemi da aka tambayeshi kam zuwan malamin.

Kwanan nan, malamin ya tattauna da tawagar yan bindiga daban-daban a jihohin Zamfara da kuma Neja don ganin sun saki mutanen da suka kama.

Sheikh Gumi ya jagoranci Malamai sun kaima tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo Ziyara
Sheikh Gumi ya jagoranci Malamai sun kaima tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo Ziyara Hoto: @OluObasanjo1
Asali: Twitter

Malam Gumi ya kuma kira yi gwamnati da su baiwa yan bindiga dama don su shiryu.

KARANTA ANAN: Ku tayani da addu'a, ina cikin kangin rayuwa har ina ji kamar na kashe kaina, Ummi Zeezee

A cewar malamin, sakamakon tattaunawar da yake yi da yan bindiga yana fidda ɗa mai ido, duk da cewa ana cikin damuwa da ayyukansu.

Ya ce kowacce tawaga tana gaya mana ƙorafin su wanda abu ne mai sauƙi. A mahangar malamin za'a iya warware waɗannan matsalolin nasu cikin sauƙi.

Sai dai waɗannn maganganun nashi sun jawo cece-kuce da dama a faɗin ƙasar, kowa na faɗin albarkacin bakinsa.

A wani labarin kuma WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan

Kwanaki kaɗan kafin zuwan watan Ramadan da kuma na ista, ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta gargaɗi musulman duniya kan dokokin kare yaɗuwar korona.

Ƙungiyar ta shawarci da su gudanar da bukukuwansu a gida tare da mutanen da suka saba rayuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262