Tafiya Landan: SERAP ta maka shugaba Buhari a Kotu kan ɓatan 3.8 Biliyan na Ma'aikatar Lafiya

Tafiya Landan: SERAP ta maka shugaba Buhari a Kotu kan ɓatan 3.8 Biliyan na Ma'aikatar Lafiya

- Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin bil'adama ta SERAP ta shigar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kotu kan ɓatan kuɗin lafiya

- SERAP ta shigar da ƙarar ne a dai-dai lokacin da shugaban ƙasar ya tafi Landan don duba lafiyarsa

- Ƙungiyar ta ce cin hanci da rashawa na neman yin katutu a ɓangaren kiwon lafiyan ƙasar nan ta yadda talaka bazai amfana ba

Ƙungiyar dake fafutukar kare hakkin ɗan adam (SERAP) ta shigar da karar shugaban ƙasa mejo janar Muhammadu Buhari a gaban kotu.

SERAP ta shigar da shugaban ƙara ne kan zargin gazawarsa wajen binciko kuɗi kimanin N3,836,685,213.13 da suka ɓata a fannin lafiya.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Kwamishinan jihar Anambra da aka Kama a Harin da aka kaima tsohon gwamna Ya Kuɓuta

SERAP ta yi iƙirarin cewa kuɗin da suka ɓata an ware su ne domin ma'aikatar lafiya, asibitocin koyarwa, Cibiyoyin kula da lafiya, da kuma hukumar kula da ingancin abinci da kwayoyi (NAFDAC).

Ƙungiyar tace dukkan wannan na ƙunshe ne a rahoton shekarar 2018 da ofishin mai bincikar kuɗi na ƙasa (Auditor) ya fitar.

Sai-dai karar ta zo dai-dai da lokacin da ake cece-kuce kan tafiyar shugaban birnin Landan domin duba lafiyarsa.

A sa'ilin da su kuma likitocin ƙasar nan suka tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani kan rashin biyansu haƙƙokin su, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/433/2021 da aka shigar satin da ya gabata a babbar kotun ƙasa dake zamanta a Abuja, SERAP ta nemi kotun da ta tilasta ma shugaba Buhari Buhari ya bincika ɓatan 3.8 biliyan kuɗin da aka ware ma fannin lafiya.

KARANTA ANAN: Yadda 'yan Biafra masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo

Sannan kuma ya binciki duk waɗanda ke da hannu wajen cin hanci da rashawa a ma'aikatar lafiya, asibitocin koyarwa, cibiyoyin kula da lafiya da kuma NAFDAC.

SERAP ta bayyana cewa cin hanci da rashawa ya mamaye fannin kiwon lafiyar ƙasar nan wanda hakan babban ƙalubale ne ga ɓangarori da dama na ƙasar nan.

Kuma hakan na nuni da kiwon lafiyar ƙasar nan zai koma hannun wasu tsirarun mutane ko kuma wata jam'iyyar siyasa.

A cewar SERAP, kididdiga da kuma bayyana yadda aka yi da kuɗin fannin kiwon lafiya a ƙasar nan ne kaɗai hanyar da talakawan ƙasar nan zasu samu kulawa mai kyau don inganta lafiyar su, da kuma daidaito a tsakanin yan ƙasar.

A wani labarin kuma Shugaban Majalisar dattijai ya gwangwaje yan kasuwar da gobara ta shafa a Jihar Yobe da abin Arziƙi

Shugaban Majalisar dattijai, sanata Ahmad Lawan ya bada gudummawar 8 miliyan ga yan kasuwar da gobara ta shafa a jihar Yobe

Sanatan ya bada wannan gudummawar ne a lokacin da yakai ziyara kasuwar don ganin abinda ya faru.

Source: Legit

Online view pixel