Shugaban Majalisar dattijai ya gwangwaje yan kasuwar da gobara ta shafa a Jihar Yobe da abin Arziƙi

Shugaban Majalisar dattijai ya gwangwaje yan kasuwar da gobara ta shafa a Jihar Yobe da abin Arziƙi

- Shugaban Majalisar dattijai, sanata Ahmad Lawan ya bada gudummawar 8 miliyan ga yan kasuwar da gobara ta shafa a jihar Yobe

- Sanatan ya bada wannan gudummawar ne a lokacin da yakai ziyara kasuwar don ganin abinda ya faru

- Ya roƙi shugabannin ƙungiyar yan kasuwar da su tabbata duk wanda gobarar ta shafa y sami wani abu daga cikin tallafin ba tare da ansa siyasa ba

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya baiwa yan kasuwar Yan Harawa da gobara ta musu ɓanna tallafin naira miliyan N8m.

KARANTA ANAN: Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky

A wani jawabi da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ezrel Tabiowo, ya fitar, ya ce sanatan ya bada wannan gudummuwa ne ya yin da yakai ziyara kasuwar dake Gashua ƙaramar hukumar bade, jihar Yobe.

A lokacin ziyarar, Lawan ya roƙi shuwagabannin kasuwar da su tabbata dukkan yan kasuwar da abun yashafa sun sami wani abu daga cikin gudummuwar da aka baiwa kasuwar ba tare da saka siyasa ba.

Shugaban Majalisar dattijai ya gwamgwaje yan kasuwar da gobara ta shafa a Jihar Yobe da abin Arziƙi
Shugaban Majalisar dattijai ya gwamgwaje yan kasuwar da gobara ta shafa a Jihar Yobe da abin Arziƙi Hoto: @DrAhmadLawan
Source: Twitter

Ya kuma tabbatar ma dan yan kasuwar cewa gwamnatin Najeriya ba zata barsu hakanan ba, zata tallafa ma waɗanda gobarar ta shafa, Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da duminsa: Mu muka baro jirgin yakin Najeriya: Yan ta'addan Boko Haram sun saki bidiyon jirgin

A jawabin da ya yi lokacin da yakai ziyara kasuwar, Ahmad Lawan yace:

"Na bada gudummuwai naira miliyan N8m. Ina fatan a raba waɗannan kuɗaɗen ga duk wanda wannan gobarar ta shafa."

"Duk gudummawar da kuka samu ku tabbata an raba an baiwa kowa da gobarar ta shafa, ba tare da duba daga wace jam'iyya mutum yake ba."

"Ina Addu'a Allah ya cigaba d kawo mana zaman lafiya a wannan yanki namu, da jihar Yobe, dama Najeriya baki ɗaya."

A wani labarin kuma Idan likitoci suka ki komawa aiki, za mu datse albashinsu, Chris Ngige

Gwamnatin Najeriya zata zartar da hukuncin dakatar da biyan likitoci matsawar basu yi aiki ba saboda yajin aikin da suka tsunduma.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ya bayar da wannan jan kunnen a ranar Juma'a a yayin da ake wata tattaunawa dashi.

Source: Legit

Online view pixel