Yanzu-Yanzu: Kwamishinan jihar Anambra da aka Kama a Harin da aka kaima tsohon gwamna Ya Kuɓuta

Yanzu-Yanzu: Kwamishinan jihar Anambra da aka Kama a Harin da aka kaima tsohon gwamna Ya Kuɓuta

- Kwamishinan jihar Anambra, Engr. Emeka Ezenwanne, da yan bindiga suka sace ya yin harin da aka kaiwa tsohon gwamnan CBN ya samu kuɓuta

- Wannan Na ƙunshe ne a wani jawabi da tawagar kamfen din tsohon gwamnan CBN ɗin ta fitar da sanyin safiyar yau Lahadi

- A ranar Talata data gabata ne wasu yan bindiga suka farmaki tsohon gwamnan ya yin da yake taro da matasa a cibiyar taro a garin Isuofia dake jihar Anambra

Kwamishinan jihar Anambra, Engr. Emeka Ezenwanne da aka kama ya samu kuɓuta, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaban Majalisar dattijai ya gwangwaje yan kasuwar da gobara ta shafa a Jihar Yobe da abin Arziƙi

An dai sace kwamishinan ne ranar Talata lokacin da wasu yan bindiga suka farmaki taron su, inda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma jigo a jam'iyyar APGA, Prof. Charles Soludo, yake taro da matasan jam'iyyar a garin Isuofia, Jihar Anambra.

A wani gajeren saƙo da aka fitar ran Lahadi wanda tawagar kanfen ɗin Charles Soludo suka fitar tare da sa hannun Christian Aburime, ya ce an saki kwamishinan ne da sanyin safiyar Lahadi.

Yanzu-Yanzu: Kwamishinan jihar Anambra da aka Kama a Harin da aka kaima tsohon gwamna Ya Kuɓuta
Yanzu-Yanzu: Kwamishinan jihar Anambra da aka Kama a Harin da aka kaima tsohon gwamna Ya Kuɓuta Hoto: @Thecableng
Asali: Twitter

Amma bai bada cikakken bayani akan yadda aka yi kwamishinan ya kuɓuta daga hannun waɗanda suka sace shi ba.

KARANTA ANAN: Ba mu Amince da ƙarin wata ɗaya kacal ba - Wata Ƙungiya ta maida ma Pantami Martani

A bayanin da Aburime ya yi bayan sakin kwamishinan ya ce:

"An ɓarke da murna da farin ciki a garin Isuofia da jihar Anambra baki ɗaya bayan sakin Kwamishinan jihar wanda wasu yan bindiga suka sace."

"Yan bindigan sun tafi da kwamishinan ne a ya yin da suka kai hari wajen taron, Prof Chukwuma Charles Soludo, a garin Isuofia, mahaifarsa."

A wani labarin kuma Buhari ya nuna bakin ciki yayinda yake juyayin rashin kakakin Afenifere Yinka Odumakin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa dangi da abokan Yinka Odumakin, sakataren yada labarai na kungiyar Yarbawa, Afenifere kan rashi da suka yi.

Har zuwa rasuwarsa, Odumakin ya kasance mai sukar gwamnatin All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel